Wednesday, December 4, 2024

Mutane 17 sun kwanta dama a wajen rububin kudi a unguwar Hausawa da ke Calabar

Manyan Labarai

Akalla mutane 17 ne ake tunanin sun kwanta dama yayin da wasu 15 suka jikkata a unguwar al’ummar Hausawa da ke layin Bagobiri a garin Calabar a ranar Talata.

Wani ganau ya bayyana cewa an ware kimanin kwanaki uku ne domin shagalin bukin nuna al’adu.

A cikin haka ne mutane suka hau wawason kudi wanda a nan ne wasu suka hadu da ajalinsu.

Bayanin yadda al’amarin ya afku

Aminiya ta nakalto majiyar na cewa:

“An kebe ranaku uku don bikin nuna al’adu ana hawa manyan babura da dai sauran al’adu.

“A lokacin da aka taru ana kallo sai wani ya bullo da mota ya watsa kudi. A wajen wawason kudik ne akalla mutane 17 suka mutu, sannan wasu fiye da 15 suna kwance a asibiti.”

Al’amarin ya afku ne da yammacin ranar kuma an kwashi wadanda suka jikkata zuwa asibitin jami’ar Calabar da asibitin sojijin ruwa.

An sallamo wadanda suka ji sauki daga bisani sannan an garzaya da wadanda suka samu karaya yankin arewa domin yi masu dorin gargajiya.

Gwamnatin jihar Cross River ta sanar da batun daukar nauyin jinyar wadanda suka jikkata.

Har ila yau, a ranar Laraba, kwamishinan yada labarai na jihar ya wakilci gwamnan jihar a ziyarar jaje da suka kaiwa al’ummar Unguwar Hausawan da lamarin ya afku.

Ya kuma bayyana cewa za su gudanar da bincike tare da daukar kwakkwaran mataki a kan lamarin.

Ya ce:

“A gaba daya abun da ya wakana, mai motar da ya yi sanadiyar afkuwar ibtila’in baya daga cikin ayarin da ya kamata su halarci wajen.”

Kwamandan hukumar hana afkuwar hadarurruka, Maikano Hassan ya tabbatar da mutuwar mutum daya.

A wani labari na daban, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya tabbatar da rasuwar Farfesa George Obiozor, shugaban kungiyar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo.

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram a daren ranar Laraba, rahoton The Punch.

Uzodinma ya ce:

“A madadin gwamnati da mutanen jihar Imo, Ni, Sanata Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo, cike da bakin ciki, ina sanar da mutuwar babban dan jihar Imo da Najeriya, shugaban Ohanaeze Ndigbo, ta duniya, Farfesa George Obiozor.

“Fitaccen malami, kwararren jakada, dattijon kasa kuma dan kishin kasa, Farfesa George Obiozor ya rasu a baya-bayan nan bayan fama da rashin lafiya.”

Duba nan: