Thursday, August 31, 2023

Sabbin Naira: Gwamnan CBN ya ki amsa gayyatar majalisa, za ta sa a kamo shi

Manyan Labarai

Abuja – Yayin da ake zaman jiran gwamnan CBN ya amsa gayyata tare da zuwa don tattauna yadda za a wankewa talakawa rai game sabbin kudi, ya ki zuwa farfajiyar majalisar wakilai.

Kakakin majalisa, Femi Gbajabiamila ya sha alwashin tura shugaban ‘yan sandan Najeriya domin ya kamo gwmanan tare da taso keyarsa zuwa farjajiyar majalisa don amsa tuhuma.

A cewar Gbajabiamila, doka ta ba mambobi da shugabannin majalisa ikon kamewa da tuhumar kowa a fadin kasar nan, The Nation ta ruwaito.

Majalisa za ta kwamushe gwamnan CBN
Za a kamo gwamnan CBN, inji majalisar kasa | Hoto: Daily Post Nigeria

Yadda batun ya fara

A tun farko dai majalisar ta nemi zama da gwamnan CBN domin tattauna batun da ke da alaka da sabbin Naira; karancinsu da kuma dalilin da yasa ‘yan Najeriya ke kokawa.

An tsara zaman a ranar Laraba 25 ga watan Janairun 2023, amma gwamnan na CBN bai halarta ba kuma bai tura wakili ba, rahoton Premium Times.

Majalisa ta matsar da zaman zuwa yau Alhamis, nan ma dai bai halarta ba, amma ya tura sakon da ke cewa yana cikin wadanda aka nada don zuwa taro kasar Senegal.

Bayan karanta wasikar, kakakin majalisa ya nuna bacin ransa, ya ce zai iya daukar matakin da ya dace daidai da abin dokar kasa ta tanada.

Batun sabbin kudi da tsoffi

‘Yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da karancin kudi a bankunan kasar nan, gashi ba sa iya saka tsoffi a asusunsu.

Yayin da wakilin News Brief Hausa ta ziyarci bankin GT a birnin Zaria, anga jama’a da yawa na layi wajen cire kudi a bakin injin ATM.

Hassan Muhammad, wani matashi da wakilinmu ya tattauna dashi ya ce:

“A barayinmu babu banki, to nazo nan don cire kudi tun bayan sallar asuba, wallahi Malam layi na tarar da yawa.

“Masu POS sai dai ka basu N100 kan kowane N1,000, ina zan iya, wannan ai bai ma taso ba.

“Ku sanar da gwamnati ta kara wa’adin nan don Allah, hakan zai taimaka mana wajen samun sauki, a taimake mu muna roko.”

Babban bankin Najeriya dai ya ce ba zai kara wa’adi ba, don Allah duk wadanda ke kudade tsoffi a kasa, su gaggauta kaiwa banki don musaya ko ajiyewa.

Kana ya ce, yana da wadatattun kudade a kasa, amma bankuna sun ki zuwa su dauka don rabawa ‘yan kasa.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: