Friday, May 31, 2024

Da Dumi-Dumi: Argentina Ta Casa Croatia, Ta Kai Wasan Karshe a Gasar Kofin Duniya 2022

Manyan Labarai

Tawagar ‘yan wasan kwallon ƙafa na kasar Argentina sun nannaga wa tawagar Croatia kwallaye a raga a wasan dab da na karshe ranar Talata.

Hazaƙar tawagar Ajentina da zakakurancin Lionel Messi da Julian Alvarez a wasan dab da na ƙarshe ya kaisu wasan karshe karo na shida a tarihi bayan nasarar da suka samu kan Croatia a filin wasan Lusail.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a halin yanzun Messi ya samu dama ta ƙarshe na jijjiga Kofin duniya a tarihinsa amma ɗan wasan gaba Alvarez ya cancanci yabo.

DUBA WANNAN: Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Bayan Ya Gano Tana Da Yara Biyu Amma Ta Boye Masa

Bayan wannan nasara da suka samu, Messi da sauran abokan wasansa yan asalin ƙasar Ajentina zasu sake dawowa wannan filin wasan kwallo ranar Lahadi su fafata da ɗaya daga cikin kasashen Morocco ko Faransa a wasan karshe.

Ba rabon ɗan baiwan Ajentina ya samu rauni a farkon fara wasan amma ya warware har ya fasa ragar abokan hamayyarssu Croatia bayan mintuna 34 da fara wasan sa’ilin da aka basu bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Alvarez ya kara kwallo ta biyu mintuna biyar bayan haka lokacin da ya karɓi kwallo daga sa kan Messi, ya samu taimako daga wasu yan wasa kafin daga bisani ya lallasa gola Livakovic.

Haka zalika Messi ya sake baiwa Alvarez kwallo bayan ya yanke zakakurin ɗan bayan Croatia Josko Gvardiol sannan ya zura wa ɗan wasan ya karisa ta zuwa cikin raga.

DUBA WANNAN: Kyakkyawar Budurwa Ta Sace Zuciyar Wani Matashi A Wajen Biki, Zai Angwance Da Ita

Yanzu dai Messi ya samu damar gyara kuskuren da suka yi wanda ya haddasa suka sha kashi a hannun tawagar yan wasan Jamus a wasan karshe na cin Kofin duniya a shekarar 2014.

A gobe Laraba idan Allah ya kaimu, za’a fafata wasa tsakanin Faransa da yan wasan Morokko waɗanda suka kafa tarihin zama kasar Afirka ta farko da ta taba zuwa wasan kusa da na karshe.

Morocco ta baiwa duniya mamaki yayin da ta haɗa wa Portugal kayansu zuwa gida da ci ɗaya mai ban haushi a wasan dab da na kusa da na ƙarshe. Faransa kuma ita ke rike da kofin wanda ta lashe a shekarar 2018.

Idon duniya dai ya yanzu ya koma kan wacce kasa ce za ta dauki wannan kofi na duniya, kamar yadda The Guardian ta dasa alamar tambaya.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: