Thursday, August 31, 2023

Mahaifi Ya Lakada Wa Diyarsa Dukan Tsiya Har Lahira Saboda Ta Kira Saurayi da Wayarsa

Manyan Labarai

Hukumar yan sandan jihar Akwa Ibom ta damke wani magidanci, Akaninyene Okokon, bisa zargin lakaɗa wa diyarsa ‘yar shekara 16 na jaki har rai ya yi halinsa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olatoye  Durosinmi, yace jami’ain Hedkwatar yan sandan Ebo sun garzaya sun kama wanda ake zargi bayan samun sahihan bayanan sirri.

Durosinmi ya faɗi haka ne yayin da yake nuna wanda ake zargi tare da wasu 195 da dakarun ‘yan sanda suka kama da zargin aikata muggan laifuka daban-daban a harabar hedkwatar ‘yan sanda da ke Ikot Akpanabia, Uyo, babban birnin jahar Akwa Ibom.

A wani bangaren kalaman kwamishinan ‘yan sandan wanda jaridar Vanguard ta tattaro, ya ce:

“A ranar 11 ga watan Disamba 2022, bayan samun wasu bayanai masu inganci, dakarun ‘yan sandan babban Ofishin Ebo suka yi ram da wani magidanci, Akaninyene Sunday Okokon.”

“Ana zarginsa da lakaɗa wa diyarsa mai suna, Abasiono Akaninyene Sunday, yar shekara 16 dukan kawo wuka har ta faɗi magashiyyan kan kawai ta dauki wayarsa da layinsa ta kira saurayinta.”

“Cikin hanzari aka kai yarinyar gidan Malami mai addu’a a kauyen Ikot Iya maimakon a kaita asibiti.”

Magidancin ya ce ba shi ya kashe yarsa ba

Yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, Akaninyene Sunday Okokon, wanda ya lakada wa diyarsa na jaki har ta mutu, ya ce ba shi ne ga halaka diyarsa ba.

Ya ce ɗiyarsa ta riga mu gidan gaskiya ne sakamakon ciwon cikin da ya kamata ba wai kamar yadda ake zargin shi ne ya yi ajalinta da duka ba.

Magidancin ya ce:

“Na lakada wa diyata duka amma ba ta rasu a lokacin da na gama zane ta. Bayan na gama dukanta ne mahaifiyarta ta gaya mun tana fama da ciwan ciki.”

A wani labarin kuma An Bankado Wasikar Soyayya Da Wata Budurwa Ta Aikewa Dan SS1, Jama’a Sun Yi Cece-kuce

Yayar yaron ta wallafa wasikar a TikTok yayin da take ja masa kunne kan harkokin makarantarsa.

Ta bukaci kanin nata ya durkusa yayin da take masa tambayoyi kan siffar marubuciyar wasikar mai suna Precious.

Duba nan: