Thursday, May 30, 2024

Aminin gwauro: Malam Daurawa ya shawarci duk mai son ya kara aure ya yi kafin shekara 10, ya fadi dalilai

Manyan Labarai

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, ya yi kira ga maza masu sha’awar kara aure da ka da su kuskura su shekara 10 da mace daya.

Daurawa, ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano, inda ya ce idan namiji ya kai wannan shekarun da mace daya, lokaci ya kure masa.

Ya ce da zaran mutum ya shekara koma da aure toh sai kasance da yarinya ‘yar shekara takwas ko tara.

Shehin malamin ya kuma ce a lokacin da ‘yar mutum ta kai shekaru 15 toh duk wacce zai auro ba za ta wuce budurwa yar shekaru 20 ba kenan babu wata tazara tsakanin amaryar da yarinyar cikinsa.

A cewarsa, matar zata samu abokiyar rigima domin yarinyar za a dunga turawa ta takalota.

Daurawa ya ce:

“Kada ka wuce shekara 10 idan za ka kara aure ba ka kara ba. Idan ka wuce shekara 10 akalla kana da ‘ya ‘yar shekara takwas ko tara.

“Da zarar ’yarka ta kai shekara 15 ba ka kara aure ba, to wacce zaka auro da wuya ta wuce shekara 20. Za ka ga tsakaninsu da ’yarka bai wuce ’yan tazarar shekaru ba.

“Saboda haka matarka ta samu abokiyar rigima. Akwai wadda za ta iya tura ’yarta ta samu amarya su rika rigima ko ta yi ta dukan amaryar saboda ta fi karfinta.

“Saboda haka wanda zai yi aure ya shirya da wuri, kuma kada duk dadin miyar mace ka ce ba za ka kara aure ba.”

Yara 102: A Karshe, Manomi Mai Jikoki 568 Ya Yanke Shawarar Daina Haifan Yara

A wani labarin kuma, wani manomi dan kasar Uganda, Musa Hasahya wanda ke da mata 12 da yaya 102 – tare da jikoki 568 – daga karshe ya yanke shawarar dena haihuwan yara baki daya.

Musa Hasahya, dan shekara 67, yanzu ya umurci matansa su fara kayyade iyalai, don su iya samun kudin siyan abinci da kula da iyalansa masu yawa.

Ya fada wa The Sun, a wata hira, cewa kudin da ya ke samu na raguwa cikin yan shekarun nan saboda tsadar rayuwa kuma iyalinsa na kara yawa.

Da ya ke magana kan aure mata da yawa, ya ce:

“Na rika auren mace daya bayan daya. Ta yaya namiji zai gamsu da mace daya?”

Duba nan: