Monday, August 28, 2023

Iyayen Amarya Sun Ki Karbar Tsoffin Kudi A Matsayin Sadakin Diyarsu A Jihar Neja

Manyan Labarai

Iyayen wata amarya a karamar hukumar Gbako ta Jihar Neja, sun nemi waliyyan mai shirin zama mijin ’yarsu da su mayar da tsoffin kudi yan N1,000 da na N5,000 da suka kai a matsayin kudin sadakin aurenta.

Daily Trust ta rahoto cewa iyayen angon sun kai kudaden ne a matsayin sadaki da na sauran saye-saye a shirye-shiryen bikin.

Duk da cewar ba a daga bikin ba, iyayen amaryar sun ce basu da bukatar kashe duka kudaden kafin nan da ranar 31 ga watan Janairu, wa’adin da CBN ya bayar na daina amfani da su.

Sun kuma yi ikirarin cewa ba su da asusun bankin da za su zuba su a ciki wanda hakan ne ya sa suka ki karbar tsoffin kudaden.

A halin da ake ciki, sun bukaci dangin angon da su tafi har zuwa lokacin da za a samu sabbin kudaden sai su dawo da shi a daura auren.

Wani dan uwan angon ya yi bayanin cewa: “Mun kai kudin sadakin gidan amaryar da dan uwanmu yake shirin aura, amma sai suka kira ni a ranar Lahadi suka ce mu zo mu karbi kudaden har sai mun sami sabbin takardun kudaden ma kawo.

“Sun ce ba su da inda za su kai tsoffin, saboda haka za mu mayar har sai mun sami sabbin.”

Ya kuma ce mutane da dama na dari-darin karbar kudaden a yankin saboda fargabar ba za su iya kashe su kafin cikar wa’adin na CBN ba.

A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya mai suna Aisha Sabi’u Bature ta amarce da hadadden saurayinta da suka hadu a soshiyal midiya.

Da take murnar bikinta a Twitter, Aisha wacce ke sana’ar siyar da sobo ta bayyana cewa angon nata mai suna Mohammed Sani Yawale, ya kasance kwastoman ta.

Duba nan: