Thursday, August 31, 2023

Shugaban Kungiyar Ibo Na Najeriya, George Obiozor, Ya Kwanta Dama

Manyan Labarai

Imo – Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya tabbatar da rasuwar Farfesa George Obiozor, shugaban kungiyar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo.

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram a daren ranar Laraba, rahoton The Punch.

 

Farfesa Obiozor
Farfesa Obiozor, shugaban Ibo. Hoto: The Cable

Gwamnan Imo, Hope Uzodinma ya yi ta’aziyyar rasuwar Obiozor

Uzodinma ya ce:

“A madadin gwamnati da mutanen jihar Imo, Ni, Sanata Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo, cike da bakin ciki, ina sanar da mutuwar babban dan jihar Imo da Najeriya, shugaban Ohanaeze Ndigbo, ta duniya, Farfesa George Obiozor.

“Fitaccen malami, kwararren jakada, dattijon kasa kuma dan kishin kasa, Farfesa George Obiozor ya rasu a baya-bayan nan bayan fama da rashin lafiya.”

KU KARANTA: Rudani A Kotu Yayin Da Wani Mutum Ya Yi Kokarin Nuna Wa Alkali Mazakutansa

Uzodinma ya cigaba da cewa:

“Mutuwar fitaccen shugaban Ibo kuma tsohon jakadan Najeriya a Amurka da Isra’ila, babban rashi na ga jihar Imo, Kudu maso Gabas da Najeriya baki daya.

“Bana haufi cewa Najeriya da kasashen duniya za su yi kewan gudumawa na ilimi da ya ke badawa da shawarwari masu amfani kan harkokin kasa da na duniya.

“Za a sanar da tsarin yin jana’izarsa nan gaba ta bakin iyalansa. Allah ya jikansa da rahama da ya gafarta masa.”

A safiyar ranar Laraba, an rika jita-jitan mutuwar dattijon kasar.

Daga bisani Shugaba Muhammadu Buhari da sauran manyan yan Najeriya sun yi ta mika sakon ta’aziyya bisa rasuwar jagoran na Ibo.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: