Thursday, August 31, 2023

Saurayi mai tsananin rowa ya yi kuskuren aikawa budurwarsa N20k sau biyu, ya nemi ta dawo masa da yan kan

Manyan Labarai

Wani matashin saurayi dan kankamo ya shiga tashin hankali bayan ya yi kuskure wajen aikawa budurwarsa kudi ta asusun bakinta.

Kamar yadda budurwar tasa ta wallafa yadda hirarsu ta gudana a TikTok ta ce ya nemi ta dawo masa da kudin da ya hau a kan wanda ya yi niyan aika mata.

Tun farko dai N20k ya so aika mata amma sai ya tura sau biyu sakamakon matsalar network da aka samu.

Sai dai kuma, a nata bangaren budurwar ta ki maida masa N20,000 din inda ta ce masa bata da kudin caji a asusunta.

Saurayin ya bukaci ta yi hakuri ta mayar masa idan ya so daga bisani zai mayar mata da kudin da za a caje ta na banki.

Ta wallafa cewa: “Sanda saurayinka dan kankamo ya tura maka kudi sau biyu bisa kuskure.”

A halin da ake ciki, ta nemi shawarar mutane kan ko ta mayar masa da kudin ko kuma a’a.

Martanin jama’a

@Victor funds: “Ki mai da masa da kudin don kada ya yanke sadakinki da zai biya.”

@bigmax196: “Lol marowaci amma ya baki kudi me yasa baki tura masa ba.”

@Gabby: “Ba dai har kin arce ba.”

@Timeyin D.: “Zan ce sau biyu a ina??? Ban gabi ba. Ka sake gwada turawa.”

Duba nan: