Thursday, August 31, 2023

Bidiyon kyakkyawar budurwa mai lalurar makanta da ta iya kitso da daurin dankwali ya ba da mamaki

Manyan Labarai

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya wacce ke da lalurar makanta amma kuma yake iya yiwa mutane kitso ta shahara.

An gano yarinyar mai suna Victoria tana aikin kitson a cikin wani bidiyo da Michael Thompson Showunmi ya wallafa a Twitter.

Duk da lalurar makanta da yake da shi, Victoria tsantsarawa abokiyar karatunta kitso mai kyau.

A dan gajeren bidiyon, Victoria ta tsaga gashin dalibar sannan ta taje shi kafin ta kitsa shi kamar mai ido.

Makauniya wacce ta iya kitso ta burge jama’a

Baya ga kitso, Victoria ta kuma iya daurin dankwalin amare, aikin da ko masu ido suke wahala kafin su yi shi.

Hakazalika tana son goyon kwalliyar zamani. A cewarta, babu abun da ba za ta iya yi ba.

An rubuta a jikin bidiyon Victoria:

“Victoria, yarinya mai lalurar makanta tana kitso, tana yiwa yan matan ajinsu kitso…ba wannan ba kawai, tana kuma daura dankwalin. Ta fada mun cewa mun dauko mai yin kwalliya a makarantarsu cewa tana son koyon kwalliya. Ta ce “idan har za a koya mun babu abun da ba zan iya yi ba”. Ina son kwazonta, zan so ku hadu da ita.”

Jama’a sun yi martani

@Brainmartin29 ya ce:

“Allah da girma yake.”

@Abiodun756:

“Babban abun al’ajabi.”

@Sunrule3:

“Ki ci gaba da aikin alkhairin.”

@makaveli18790:

“Hakan ya yi kyau.”

Duba nan: