Thursday, May 30, 2024

Zaben 2023: Jerin Jihohi 10 Mafi Zaman Lafiya a Najeriya

Manyan Labarai

Yayin babban zaben Najeriya ke kara gabatowa, kasar na cike da tsoro da fargaba saboda matsalar rashin tsaro da ya yi katutu a cikinta.

Matsalar rashin tsaro ya zama ruwan dare a fadij yankunan Najeriya kuma ana fargabar kada lamarin ya kara tabarbarewa a lokacin zabe wanda za a yi a watan gobe.

Yayin da yankunan arewa maso yamma, arewa ta tsakiya da kudu maso yamma ke fama da matsalolin yan bindiga da masu garkuwa da mutane, yankin kudu maso gabashin kasar na fama ne da ta’addancin kungiyar awaren IPOB inda kuma arewa maso gabas ke fuskantar matsalar Boko Haram da ISWAP.

Wani sabon binfice da Satisense ya saki a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu ya nuna adadin mutanen da aka kashe a jihohin Najeriya cikin shekarar 2022.

Kamar yadda Satisense ya rahotk, jihohi 10 ne kawai suke zaman lafiya cikin jihohi 36 na Najeriya.
Wadannan jihohi sun hada da biyar na arewa da kuma wasu biyar na kudu.

Jahar Ekiti ce ta fi koina zaman lafiya kasancewar mutum shida kawai ne suka kwanta dama ta dalilin rashin tsaro a 2022.

Ga cikakkun jerin jihohin a kasa:

1. Jihar Ekiti

2. Jihar Gombe

3. Adamawa

4. Kano

5. Jigawa

6. Nasarawa

7. Akwa Ibom

8. Bayelsa

9. Oyo

10. Osun

Duba nan: