Thursday, August 31, 2023

Kotu Ta Dakatar da Hukumar DSS Daga Kama Shugaban INEC

Manyan Labarai

Wata babbar kotun tarayya ta dakatar da karar da ke neman a tsige Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu daga mukaminsa kan zargin ba da bayanan karya a kan kadarorinsa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a M. A. Hassan ya ki amincewa da bukatar da wasu 14 da masu karar suka gabatar a ranar Laraba, 4 ga watan Janairu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Mai shari’an ya ce bayanan da Yakubu ya bayar dangane da kadarorin da ya mallaka yana bisa doka, don haka ya ki amincewa da karar da aka shigar kan shugaban na INEC.

Hakazalika, alkalin ya hana hukumar DSS, rundunar yan sandan Najeriya da Hukumar kula da Da’ar Ma’aikata (CCB) kama Yakubu.

Wannan hukunci ya biyo bayan karar da wani mai suna da Somadina Uzoabaka ya shigar da Yakubu da kuma Babban Lauyan Kasa, yana neman Shugaban INEC ya ajiye mukaminsa ya koma gefe har zuwa lokacin da za a kammala binciken tuhume-tuhumen da ke kansa.

Har ila yau, wanda yake karan ya kuma bukaci kotu ta haramta wa shugaban INEC rike kowane irin mukamin gwamnati na tsawon shekara 10.

Da yake maida martani kan karar, Farfesa Yakubu, ya gabatar wa kotun cikakkun bayanai da hujjojin da suka tabbatar wa kotun hanyoyin samun kudinsa halastattu ne.

Magoya Baya Sun Nemi Atiku, Obi da Kwankwaso Su Janye Daga Takarar Shugaban Kasa a 2023

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa kasa da watanni biyu gabanin babban zaben shugaban kasa dake tafe a 2023, sananniyar kungiyar magoya bayan Bola Tinubu, Tinubu/Shettima Network (TSN) ta yi kira ga sauran masu neman zama shugaban kasa su janye wa dan takarar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban kungiyar TSN na kasa, Dakta Kailani Muhammad, ne ya yi wannan kira jiya Alhamis a wurin rantsar da shugabannin kungiyar na matakin kasa da kuma kaddamar da hedkwata a birnin tarayya Abuja.

Injiniya Kailani ya bukaci masu hangen zama shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, na Labour Party, Peter Obi, na NNPP mai kayan marmari, Rabiu Musa Kwankwaso, da sauransu da su janye wa Bola Tinubu, su daina asarar karfin su da dukiyarsu a wurin kamfe.

Duba nan: