Rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da cafke Chiroman Barayan Zazzau, Shehu Umar tare da tsare shi a kan zargin aikata luwadi da wani yaro mai shekaru 14.
Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Muhammadu Jalige, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a Zaria, jihar Kaduna a ranar Laraba, Daily Nigerian ta rahoto.
Jalige ya kuma ce za a gurfanar da wanda ake zargin da zaran an kammala bincike.
Yayan wanda abun ya ritsa da shi, Hamza Zubairu, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa lamarin ya afku ne a ranar 9 ga watan Disamba a yankin Kwarbai da ke garin Zariya.
Mista Zubairu ya ce mutane na ganin mutuncin wanda ake zargin, wanda makwabci ne ga iyayen yaron da aka yiwa fyaden sosai.
Ya kara da cewar a wannan rana da abun zai faru, wanda ake zargin ya tura yaron dakinsa ya dauko masa wasu kudade amma sai ya bisa cikin dakin sannan ya rufe kofa.
Sai basaraken ya fito da wuka sannan ya yi barazanar kashe yaron idan har ya yi ihu a kan abun da yake shirin aikata masa.
Ya ce da farko yaron ya shiga tashin hankali kuma ya kasa fada ma kowa abun da ya faru da shi har sai daga bisani sannan ya samu karfin gwiwar fadama kanwar mahaifinsa.
“Kanwar mahaifin nasa ce ta kai rahoton lamarin ga hedkwatar yan sanda a Zariya,” in ji Zubairu.
Da take jawabi, Aishatu Ahmed, shugabar sashin kula da cin zarafin mata da yara na asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya, ta ce cibiyar ta samu takarda da ke bukatar yiwa yaron gwaje-gwaje.
Ta ce sun tura sakamakon bincikensu hedkwatar yan sanda da ke Zariya.
Aishatu ta ce: “Jami’an ’yan sanda da ke Fada, Zariya sun kawo yaron don a duba lafiyarsa, tare da wadda ake zargin ya aikata fyaden kuma mun bai wa ’yan sanda sakamakon bincikemmu.”
A wani labarin, wasu matasa 19 sun shiga hannun Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, kan kokarin hada auren jinsi daya a jihar.
Wadanda aka kaman, wadanda mafi yawansu mata ne sun yi kokarin daura wa wasu maza biyu masu suna Abba da Mujahid aure a matsayin mata da miji.