Friday, May 31, 2024

Rabin Masu Sana’ar POS A Najeriya Sun Dena Saboda Karacin Naira

Manyan Labarai

An gano cewa sama da kashi 50% na masu sana’ar POS sun rufe kasuwancinsu saboda karancin sabbi da tsofaffin kudaden Naira, rahoton Punch.

Hussein Olanrewaju, babban jami’in tara kudi na kasa na kungiyar hada-hadar kudi ta wayar salula kuma wakilan bankuna a Najeriya, ya bayyana a ranar Litinin da ta gabata cewa karancin kudi na sabbi da tsohon Naira ya kara ta’azzara matsalolin da mambobinsu ke fuskanta.

POS

Ya bayyana cewa ya kamata wakilansu su samu sabbin takardun kudin ciki sauki, amma kuma ya nuna rashin jin dadinsa da yadda wasu ‘yan Najeriya ke cin gajiyar lamarin ta hanyar karbar kudaden da ya wuce kima.

Ya ce:

“Masu gudanar da ayyuka kamfanoni ne masu lasisi da ke ba da dandamali ga wakilai don amfani da su. A halin yanzu, wakilai ba sa samun kulawa ta musamman kuma a sakamakon haka, sama da kashi 50 cikin dari na shagunan su an rufe su.”

 

“Duk da haka, wasu jami’an suna yin iya kokarinsu don siyan kudin, yayin da wasu ke kashe makudan kudade daga Wannan ATM zuwa wancan, wanda hakan ya sa kudin sabis ya karu.”

“Yana da kyau a lura cewa wasu ‘yan Najeriya na cin gajiyar wannan lamarin ta hanyar karbar kudaden da ba su dace ba.”

Hussein ya jaddada cewa manufar da ake amfani da ita na musayar kudade a wuraren da ba na banki ba ba lalle yakai ga cimma bukataba saboda karancin wakilai da aka zaba domin shirin.

Ku Karanta: EFCC Ta Kama Manajan Banki a Abuja Da Ya Boye N29m Na Sabbin Kudi

Ya kuma kara da cewa kara yawan wakilai shine mafita mafi inganci don rage wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

“Kamar yadda babban bankin CBN ya shirya, shirin na tafiya yadda aka tsara, amma ba ya samar da riba ga wakilan, daga cikin wakilai miliyan 1.4, 30,000 ne kawai aka zabo don shiga shirin musayar kuɗin, wanda adadin ya yi kadan wajen kawo gagarumin sauyi.”

Daga karshe ya ce:

“Wakilai su ne wadanda ke da damar da za su iya saukaka wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fama da su.”

 

Duba nan: