Wednesday, May 29, 2024

Daga siyan soborodo, mai sobo ta yi wuff da kwastoma

Manyan Labarai

Wata matashiya yar Najeriya mai suna Aisha Sabi’u Bature ta amarce da hadadden saurayinta da suka hadu a soshiyal midiya.

Da take murnar bikinta a Twitter, Aisha wacce ke sana’ar siyar da sobo ta bayyana cewa angon nata mai suna Mohammed Sani Yawale, ya kasance kwastoman ta.

Aisha ta wallafa katin gayyatar aurenta tare da hirarsu da Mohammed.

Ma’auratan sun shiga daga ciki ne a ranar Asabar, 7 ga watan Janairun 2023 a jihar Katsina.

Ta rubuta a shafinta “Daga siyan Zobo & Kunun Aya #WhatABlesaedRamadan na auri kwastoma na.

“#ATwitterMukaHadu.”

Jama’a sun yi martani

@ImamShams: “Shin akwai mai siyar da zobo da kunan aya kuma? Akwai bukatar na siya haajarsu yanzun nan.”

@nafdak: “na taya ku murna. Allah ya albarkace ku. Yanzu ya zama mai hannun jari.”

@usmanomolara3: “Kuma irin wannan kasuwancin nake yi faaa amma za mu ci gaba.”

@Abumazeedah2: “Mazaa na ga soyayyarka fa Zobo bai da iyaka, na roki Allah ta’ala ya baku zaman lafiya a gidanku.”

@es_aderm: “Allah yha sa albarka. Nima kwanan nan zan fara siyar da zobo.”

@BelloMB96: “Mutumina ya samu sobo da Mai sobo. Allah ua vada zaman lafiya.”

@UmmahAli: “A matsayina na shugabar kungiyar masu siyar da zobi, ina rokon Allah ya albarkaci aurenku.”

Duba nan: