Friday, May 31, 2024

Yanzu-Yanzu: Daga Karshe, Obasanjo Ya Mara Wa Peter Obi Baya, Ya Bayyana Dalili

Manyan Labarai

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya fito fili ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, gabanin zaben shugaban kasa na Fabrairun 2023.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a sakonsa na sabon shekara mai taken ‘kira ta ga yan Najeriya musamman matasa.’

 

Obasanjo da Obi
Obasanjo ya goyi bayan Peter Obi a zaben 2023. Hoto: Daily Post

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa babu waliyyi cikin yan takarar shugaban kasar, amma idan ana batun ilimi, ladabtawar da abin da za su iya yi, Obi na gaba da sauran, Daily Trust ta rahoto.

Babu waliyyi cikin yan takarar shugaban kasa amma Obi ya fi sauran – Obasanjo

Obasanjo, cikin sakon da ya rattaba hannunsa ya ce:

KU KARANTA: Mambobin APC Sama da 10,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Wurin Gangamin Atiku Na Nasarawa

“Babu waliyyi cikin yan takarar amma idan aka kwatanta abin da suka yi a baya, fahimtarsu, ilimi, da lafiya da abin da za su iya yi musamman duba da inda kasar ta tsinci kanta yau da kwarewata kan aikin da nima na yi, Peter Obi, wanda na ke matsayin mai koyarwa a wurinsa shine ke kan gaba.

“Sauran kamar sauran mu suna da rawar da za su taka don ceto Najeriya. Wani abu mai muhimmanci game da Peter shine tamkar allura ya ke da ya hada arewa da kudu kuma ba zai bata ba.

“Ba sai an fada ba, yana da mutane da za su iya jan kunnensa, a lokacin da bukatan hakan ya taso. Ba sai an fada ba yana da matashi ne wanda ya dauki abokin takara mai tsaftaccen tarihi da nasarori a bayyane da boye.”

Tushe: News Brief Hausa

Dakaci karin bayani …

Duba nan: