Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga wasikar soyayya da wata yarinya ta rubutawa matashi dan aji hudu a Sakandare mai suna Somto.
Yayar yaron ta wallafa wasikar a TikTok yayin da take ja masa kunne kan harkokin makarantarsa.
Ta bukaci kanin nata ya durkusa yayin da take masa tambayoyi kan siffar marubuciyar wasikar mai suna Precious.
Budurwar ta ce bata yi soyayya da kowa ba lokacin da take SS1. Kanin nata na ta dariya yayin da yake sifanta budurwa tasa wacce ta rubuto masa wasikar.
Ya bayyana cewa sun shafe tsawon watanni shida suna soyayya.
Precious na so ta aure shi
Precious ta bashi hakuri a kan rashin sumbatarsa, tana mai cewa ta yi hakan ne saboda basu dade da fara soyayya ba.
Ta kara da cewar ba za ta iya sumbatarsa a harabar gidansu ba. Precious ta yi bayanin yadda take kewar Somto sannan ta shawarce shi da ya mallaki waya don taimakawa soyayyarsu.
Budurwar ta bayyana shirinta na son aurensa sannan ta bukace shi da ya yaga wasikar bayan ya gama karantawa.
Jama’a sun yi martani
Victor Chukwuebuka ya ce: “Nima a SS1 nake kuma ina da budurwa mahaifiyata ta san da batun amma mahaifina na ta ihu kuma na fada masa ya yi rayuwarsa don nima nayi tawa.”
Isabella ta ce: “Haaaaa yaran nan sun fara abubuwa lokacin da nake ss1 kashe mu ake yi da karatu.”
Uncle_Simple_ ya ce: “Mahaifiya ta tsinci wasikar soyayya a aljihun kanina yana cewa yana kaubar blessing kamar yadda maza ke son shinkafa mahaifiyata tace ba karamin soyayya ba.”
kaykay ya ce: “Awwww wannan ya yi kyau, kawai ki karfafa masa gwiwa sannan ki koya masa aikata daidai don kada ya boye maki abubuwa.”
Hajiaminat02 ta ce: “Kanina ya gabatarwa mahaifiyata da wata yarinya a lokacin da ta ziyarce shi a makaranta cewa suna soyayya.”
AYOMIKUN ta ce: “Naki ya ma fi….nawa kanin ya kawo budurwarsa gida sannan ya fada mun na bar daki na koma falo.”
A gefe guda, wata kyakkyawar budurwa ta wallafa wani bidiyon zolaya a TikTok inda ta tunkari wani matashi sannan ta bukaci lallai ya furta mata soyayya.
Matashiyar mai suna Phoebe ce ta wallafa bidiyon kuma zuwa ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba, ta samu mutum 428k da suka kalla.