Thursday, August 31, 2023

Gobara Ta Yi Ajalin Liman, Matarsa Da Yaransa Biyu a Zariya

Manyan Labarai

Hukumar kwana-kwana ta jihar Kaduna ta ce wata Gobara da aka wayi garin Jumu’a da ita ta yi ajalin wani bawan Allah mai suna, Muhammad Sani da iyalansa a Zariya.

Hukumar ta bayyana cewa wutar ta lakume rayukan mutumin da matarsa, Raulatu Sani, da dansu namiji, Hashim Sani da karamar yarinya da ake goyo, Fatima Sani.

Kwamandan hukumar mai kula da shiyyar Zariya a jihar Kaduna, Mohammad Umar, shi ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai ranar Jumu’a a garin Zariya.

Umar ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 1:00 na tsakar dare a Hajiya Maituwo St., Low-Cost Area Zaria, karamar hukumar Zaria, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa an kira jami’an hukumar kwana-kwana ne bayan wutar ta cinye sashin da iyalan suke zama a cikin gidan.

Sai dai duk da haka, Kwamandan ya yi bayanin cewa hanzarin kai daukin jami’an hukumar ya dakile yuwuwar yaduwar wutar zuwa gidajen Makota a Anguwar.

Wani Ganau, Safiyanu Aliyu, ya shaida wa hukumar dillancin labarai ta kasa watau NAN cewa marigayi Sani, Limami ne a daya daga cikin Masallatan Layin Buhari dake Low Cost, Zariya.

Aliyu, duk da bai bayyana makasudin tashin gobarar ba, ya ce sun ji sanarwa daga Yan sa’kai da ke kokarin ba da tsaro a yankin na cewa Gobara ta tashi a Anguwar.

Ya kara da cewa lokacin da suka hito domin kai agaji sai suka taras wutar ta cinye sashin da iyalan gidan suke zaune.

Yace tuni aka kai gawar mamatan asalin gidan iyayensu da ke Dogarawa, karamar hukumar Sabon Gari domin a musu Janaza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

A wani labarin kuma Dan China Da Ake Zargi Da Kisan Ummita Ya Ce Ya Kashe Mata Miliyan N60

A ranar Laraba, 11 ga watan Janairu ne mutumin kasar Chinan nan mai suna, Frank Geng Quangrong, wanda ake zargi da kisan masoyiyarsa yar jahar Kano Ummukulsum Sani, wacce aka fi sani da Ummita, ya fara kare kansa a kotu.

Quangrong ya sanar da kotu cewa shi Musulmi ne kuma ya na aiki a wani kamfanin tufafi a kasuwar Kantin Kwari da ke jahar Kano.

Duba nan: