Wata babbar kotun tarayya ta zartar da hukuncin daurin shekaru 235 a gidan yari ga wani matashi kan aikata zamba.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ce ta gurfanar da mutumin a ranar 2 ga watan Yulin 2019 kar kashin jagorancin Mai Shari’a Jude Okeke.
Alkali ya kama shi da laifuka 45 da ake tuhumarsa a kai
Aminiya ta rahoto cewa hukumar ta Efcc tana tuhumarsa da aikata laifuka 45 da suka hada da sata, halasta kudin haram, damfarar yanar gizo da kuma hadin baki, wadanda suka sa kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara 235.
Da farko wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa a kai, lamarin da ya sanya shari’ar daukar tsawon shekaru ana fafatawa.
Daga baya, alkalin ya ce ya gamsu da hujojjin da aka gabatar wa kotun inda ya ce ta kama wanda ake zargin da laifi sannan ta yanke masa hukuncin daurin.
Kotun ta ce laifin ya yi karo da sashe na 321(1) na kundin laifuka na Jihar Oyo na shekarar 2003.
Mahaifi Ya Lakada Wa Diyarsa Dukan Tsiya Har Lahira Saboda Ta Kira Saurayi da Wayarsa
A wani labarin, hukumar yan sandan jihar Akwa Ibom ta damke wani magidanci, Akaninyene Okokon, bisa zargin lakaɗa wa diyarsa ‘yar shekara 16 na jaki har rai ya yi halinsa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olatoye Durosinmi, yace jami’ain Hedkwatar yan sandan Ebo sun garzaya sun kama wanda ake zargi bayan samun sahihan bayanan sirri.
Durosinmi ya faɗi haka ne yayin da yake nuna wanda ake zargi tare da wasu 195 da dakarun ‘yan sanda suka kama da zargin aikata muggan laifuka daban-daban a harabar hedkwatar ‘yan sanda da ke Ikot Akpanabia, Uyo, babban birnin jahar Akwa Ibom.
A wani bangaren kalaman kwamishinan ‘yan sandan, ya ce:
“A ranar 11 ga watan Disamba 2022, bayan samun wasu bayanai masu inganci, dakarun ‘yan sandan babban Ofishin Ebo suka yi ram da wani magidanci, Akaninyene Sunday Okokon.”
“Ana zarginsa da lakaɗa wa diyarsa mai suna, Abasiono Akaninyene Sunday, yar shekara 16 dukan kawo wuka har ta faɗi magashiyyan kan kawai ta dauki wayarsa da layinsa ta kira saurayinta.”
“Cikin hanzari aka kai yarinyar gidan Malami mai addu’a a kauyen Ikot Iya maimakon a kaita asibiti.”