Thursday, May 30, 2024

Matashi Ya Siya Hadaddiyar Motar Benz, Ya Yi Anko Da Ita a Bidiyo

Manyan Labarai

Wani matashin saurayi wanda ya siya dalleliyar motar Marsandi Benz sabuwa a leda ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Matashin miloniyan mai suna @sanousasawadogo ya garzaya yanar gizo don saki wani bidiyonsa yayin da abokai ke taya shi murnar wannan babban nasara da ya samu a rayuwa.

A dan gajeren bidiyon da ya wallafa a manhajar TikTok, an gano shi tsaye a gaban motar sanye da wani kaya da ke dauke da logon Benz wanda ke nuna anko ne ya yi don banbanta cewa shine mamallakin motar.

Duk a cikin bidiyon mai ban dariya, an gano inda masu yi masa fatan alkhairi suka kewaye motar yayin da aka saka ta a tafiya kadan-kadan.

Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun bayyana cewa lallai wannan lamari ne na ‘dan kauye ya sai agogo’ yayin da suke al’ajabin wani irin aiki yake yi da har ya iya mallakar motar.

Abun da mutane ke cewa:

A nan mun tattaro maku wasu daga cikin martanonin jama’a a kan wannan matashi bayan sun kalli bidiyon.

Omos: “Gayena ya saka rigarsa dauke da logon benz.”

Nasa Austin: “Ga wata motar a hannun da bata dace ba.”

Toretto: “Ga wani a Amurka yana kewar motar Marsandi lmao.”

Face: “Ainahin abun da ake nufi da kana iya kasancewa da kudi kuma ya zamana baka da matsayi.”

Victory: “Abu ya kai kanka ka dinka janpa da wando da logon benz.”

Carlitos way: “Sun gwammaci su mallaki hadaddiyar mota maimakon gida mai kyau! Haka abun yake a nan US.”

Duba nan: