Thursday, May 30, 2024

Tarihin Masarautun Arewa: Jerin Manyan Sarakuna 10 na Arewacin Najeriya

Manyan Labarai

Yankin Arewacin Najeriya yanki ne da Allah ya albarkace shi da sarakuna da dama. Sarakuna su ne iyayen al’umma kuma su ne ginshikan al’umma.

Hakazalika, Sarakuna na da matukar kima a idon jama’arsu, tambaya anan; su waye manyan sarakuna 10 na Arewacin Najeriya? Kuma Menene matsayin Su? Ku biyo ni domin sanin su waye wadannan Sarakuna

  1. Sarkin Ilorin

Akasarin mutane ba sa daukar Ilorin a matsayin wani bangare na arewa,’ Sai dai kuma ya kasance gari ne mai matukar muhimmanci a Arewacin Najeriya.Inda yake dauke da yawan yaren Yarabawa da kuma Baruba, Masarautar Illorin masarauta ce da ta taka rawa a Jihadin Musulunci a shekarar 1804 bayan nan ne Abdusalami dan Salih Alimi, ya zama sarki a shekara 1824 wanda ya fito daga kabilar fulani.

Zuwan Turawan Ingila wanda, su ma sun dauki Sarkin Ilorin a matsayin daya daga cikin manyan Sarakuna 10 a Arewacin Najeriya, kambun da Masarautar ke rike da shi har ila yau.

Sarkin Ilorin na yanzu shi ne Ibrahim Sulu Gambari, babban lauyan lauyoyin na Najeriya, ya kasance sarkin da aka nada a shekarar 1995 a matsayin sarki na 11 a masarautar Ilorin a jihar Kwara wanda yafito ne daga gidan sarautar Fulani kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Kwara. Yana daya daga cikin manyan sarakuna goma daga arewacin Najeriya.

  1. Etsu Nupe

Etsu kalmar Nupe ce ta ‘Sarki’, ma’ana Etsu Nupe shi ne sarkin dukan mutanen Nupe, mai hedikwata a Bida. Don haka, a jerin sarakunan Arewacin Najeriya, Sarkin Bida shi ne na 9 a jerin sunayen.

Bayan faduwar Masarautar Nupe da ta gabace ta, Masarautar Bida ta koma karkashin masarautar Gwandu, hedkwatar masarautar Sokoto.  Usman Zaki dan Malam Dendo, Bafulatani ne, ya zama sarki na farko a masarautar Nupe a shekarar 1835.

Etsu Nupe na yanzu shi ne Alhaji (Dr) (Brig. Gen) Yahaya Abubakar rtd GCFR, soja mai ritaya, dattijon jiha, kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Neja, wanda hakan ya sa ya kasance daya daga cikin manyan sarakunan arewacin Najeriya.

  1. Sarkin Bauchi

Kafin Jihadin shekarar 1804, kananan kabilu masu zaman kansu suke mulkin yankin jihar Bauchi.  inda aka samu sauyin hakan a shekarar 1805, inda Yakubu I dan Dadi,wanda ya kasance daya daga cikin daliban Shehu Dan Fodio ya nada kansa a matsayin Sarkin Bauchi na farko, inda a da aka yi masa lakabi da Lamido. Wannan ne ya sa a yanzu ake wa Masarautar lakabi da ‘Bauchin Yakubu.

Masarautar Bauchi tana daga cikin manya-manyan masarautu 10 a Arewacin Najeriya, ta sami wannan martaba ne tun zuwan Turawan mulkin mallaka.

Dokta Rilwan Suleiman Adamu, wanda shine sarki na yanzu ya kasance Da ne ga tsohon sarki, Sulaiman Adamu, wanda ya rasu a shekarar 2010 bayan ya shafe shekaru 28 yana mulki.Dokta Ridwan ya kasance shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Bauchi,Duk da kasancewar akwai manyan masarautu masu dimbin tarihi a jihar; kamar masarautar Katagum, Jama’are, wanda suna daya daga cikin sarakunan da suka dade a kan karagar mulki a arewacin Najeriya.

  1. Sarkin Zazzau

Masarautar Zazzau na daya daga cikin Asalin masarautu Bakwai na Hausa wanda Bayajidda ya assasa kuma ‘ya’yansa suka mulka. Masarautar zazzau babbar masarauta mai dimbin tarihi.  Masarautar Zazzau tana da manyan sarakunan tarihi, irin su Sarauniya Amina, Sarki Makau, Sarki Jatau, da dai sauransu.

Baya ga kasancewarta daya daga cikin manya-manyan masarautu 10 a Arewacin Najeriya, ta kasance tana da da tarihi mai sarkakiya, inda Sarkin masarautar suka kasu zuwa gidaje hudu Katsinawa, Mallawa, Bare-bari, da Sullubawa. Inda Sarki na yanzu, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, ya fito daga gidan Mallawa,wanda shi ne na farko tun bayan shekaru Dari.

Masarautar ta zazzau tana cikin sahun gaba a jerin manyan sarakuna.Kasancewar ta a yakin Babban Birnin Arewacin Najeriya na lokacin wanda hakan ya ba wa Sarkin daraja sosai. Sarkin Zazzau a lokacin, Ja’afaru Dan Isiyaku,ya kasance daya daga cikin majalisar sarakunan yankin Arewa.

  1. Sarkin Katsina

Masarautar Katsina na daya daga cikin tsoffin masarautu a arewacin Najeriya, inda sarkin ya kasance daya daga cikin manyan sarakuna 10 a arewacin Najeriya.

Masarautar ta hadu da masarautar Sokoto ne a lokacin da Ummarun Dallaje, uban masarautar Dallazawa, inda Shehu Usman Danfodio ya mika masa tuta.Inda Sarkin na yanzu ya fito ne daga daular Sullubawa, wadda aka kafata a lokacin da Muhammadu Dikko ya zama sarkin Fulani na tara a shekarar 1906.

A cikin Sarakunan Arewacin Najeriya, Sarkin Katsina yana da matsayi mai girma. Haka kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na yankin ku wanda ke rike da mafi yawan Hakimai a Najeriya.

  1. Lamidon Adamawa

A tarihin martabar Sarakuna a Arewacin Najeriya, Lamidon Adamawa ya tsaya tsayin daka. Masarautar Adamawa a da ta kasance a yankin Fombina ne,wanda a yanzu ta ke a Adamawa, da kuma wasu sassan Taraba, Kamaru, da Chadi. Yana daya daga cikin mafi girman masarauta wancan lokaci.

Modibo Adama shi ne ya kafa Masarautar a shekarar 1809, wanda ya kasance Dalibin Shehu Dan Fodio ne a lokacin da ya ci Masarautar Mandara da yaki. Ya yi mulki na tsawon shekaru 40 inda zuriyarsa ce suka gaje shi, har zuwa yanzu.

Karfin mulkinsa ne ya sanya shi kasancewa cikin manyan sarakuna 10 na arewacin Najeriya. Sannanen Lamidon Adamawa,Aliyu Mustafa Barkindo, ya yi mulki na tsawon shekaru 57, wanda ya rasu a shekara ta 2010, ya rasu yana da shekaru 88. Jana’izar sa ya samu halartar gwamnonin jihohi sama da 20 da sauran manyan jami’an tsaro. Ɗansa, Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, shi ne ya gaje shi, kuma ya kasance lamidon Adamawa na 12. Kuma a yanzu Shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar.

  1. Sarkin Kano

An kafa Masarautar Kano ne a shekarar 1805 a lokacin zuwan Musulunci.Kafin nan, kasar Kano,ta kasance daya daga cikin kasashen Hausa tun asali, ta kafune tun shekarar 999, lokacin da Bagauda ya zama Sarkin Kano na farko. Masarautar Kano ta kasance masarautar da ta taba cin turawan Ingila da yaki a yaƙe-yaƙe uku da akayi har zuwa lokacin da ta fadi a shekara ta 1903,inda a sannan ne aka kori Sarki Aliyu Babba.

Masarautar Kano ta kasance daya daga cikin manyan masarautu a Najeriya.Yayin da Sarkin Kano na daya daga cikin manyan sarakunan da aka fi sani kuma mai matsayi mafi girma a cikin Sarakunan Arewacin Najeriya.

Kafin kafa sabbin masarautu guda 4 a jihar, jihar Kano ce kadai jihar da take da masarautu daya in aka cire jihar Sokoto. Yanzu jihar tana da masarautu masu daraja ta daya har guda 5. Marigayi Ado Bayero, wanda ya kasance Sarkin Fulani na 13, ya kasance daya daga cikin sarakunan da suka dade a kan karagar mulki kuma aka fi sanin su a Najeriya, kuma ya yi mulki na tsawon shekaru 52.

  1. Sarkin Gwandu

Nasan Jama’a za su yi mamaki sosai amma Sarkin Gwandu na daya daga cikin manyan sarakunan arewacin Najeriya Duk da yake wannan Masarautar ba ta da Suna kamar sauran masarautu. Masarautar da ke a garin Gwandu na jihar Kebbi a yau,ta kasance daya ne daga cikin manyan biranen masarautu da suka fito daga Sokoto.

Bayan Jihadi, Dan Fodio ya raba Sarautar Sokoto tsakanin dansa Muhammadu Bello da kaninsa Abdullahi. A lokacin Gwandu shi ne babban birnin gabas, inda sarakuna da dama suka yi mubayi’a.

  1. Shehun Borno

Masarautar Borno ita ce ta biyu a cikin manyan sarakunan Arewacin Najeriya. An kafa Masarautar ne a farkon karni na 20 wacce ta zama daular Bornu, wacce ta kasance tun shekaru1000 da suka gabata.

Daular El-Kanemi mai mulki a yanzu, ta samo asali ne daga Muhammad El-Kanemi, wanda ya yi mulki tsakanin 1809-1837. Daular Borno daula ce da ba a taba cin ta da yaki ba. Musulunci ya shigo yankin ne tun a karni na 11, kuma Borno ta kasance cibiyar koyon addinin musulunci tun karni na 17.

Shehun Borno na yanzu,Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanem, ya fito daga zuriyar wanda ya kafa Masarautar El-Kanemi .Ya hau mulki ne tun shekarar 2009 kuma yana daya daga cikin manya-manyan sarakuna a arewacin Najeriya, Wanda ya kasance Mataimakin Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), babbar kungiyar Musulunci a Najeriya, kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa.

  1. Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi shi ne Sarki mafi muhimmanci a Arewacin Najeriya, kuma shi ne jagoran musulmai kusan miliyan 100 na kasar, wanda aka fi sani da “Sarkin Musulmi” Wannan hakan ya sa ya zama Sarki mafi tasiri kuma kan gaba a cikin manyan mukamai na Sarakunan Arewacin Najeriya. kuma shi ne shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (Society for the Support of Islam – JNI), kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) da kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Arewa.

Duba nan: