Thursday, November 7, 2024

Da Dumi-Dumi: Argentina Ta Lallasa Faransa, Ta Lashe Kofin Duniya 2022

Manyan Labarai

Tawagar yan wasan kwallon kafa na ƙasar Argentina sun samu galaba kan ƙasar Faransa a ƙayataccen wasan karshe da suka fafata da yammacin ranar Lahadi.

Daily Trust ta rahoto cewa Argentina ta samu nasara da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga wanda ya bata damar lashe kofin duniya na bana 2022.

Wasan ƙarshen wanda ya yi zafi sosai tsakanin ƙasashen biyu ya ƙare da ci 2-2 bayan mintuna 90. Haka zalika an tashi wasan 3-3 bayan ƙarin mintuna 30 domin tantance zakara.

News Brief Hausa ta tattaro cewa ba’a iya gane mai nasara ba har sai da Alƙalin wasa ya ce a tafi bugun daga kai sai mai tsaron raga.

DUBA NAN: Da Dumi-Dumi: Argentina Ta Casa Croatia, Ta Kai Wasan Karshe a Gasar Kofin Duniya 2022

Tun a farkon wasan, fitaccen ɗan kwallon kafa na duniya, Lionel Messi ne ya fara jefa kwallo a ragar Faransa bayan ƙetar da Alkali yace Dembele ya yi wa Di Maria a minti na 23 da fara taka wasan.

Angel Di Maria ya kara kwallo ta biyu a ragar Faransa a minti na 36 da fara wasan amma zakarun 2018 sun farfaɗo mintuna 10 kafin busa tashi, inda Kylian Mbappe ya rama duka kwallayen biyu cikin abinda bai wuce mintuna biyu ba.

Mbappe, ɗan shekara 23 a duniya ya farke kwallo ɗaya ne a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 80 ana gab da tashi kana ya farke ta biyu a minti ɗaya kacal bayan haka, lamarin da ya tilasta buga karin lokaci.

Messi ya sake leƙa zaren Hugo Llorin na ƙasar Faransa ya sake jefa Argentina a gaba amma Faraɓsa tace ba zai yuwu ba ta sake farke kwallon ta hannun Mbappe wanda ya samu nasarar jefa kwallo uku rigis a wasan.

DUBA NAN: Na Kawo Canji, Na Yi Bakin Kokarina a Matsayin Shugaba, Inji Buhari

Duk da Mbappe zai samu kyautar ɗan wasna ya fi kowa zura kwallo a raga, ya yi iya bakin kokarinsa don ganin sun sake ɗaukar Kofin karo na biyu a jere.

Da sun samun nasara, Faransa zata shiga jerin kasashen da suka taɓa lashe kofin sau biyu a jere bayan nasarar da suka samu a gasar baya wacce ta gudana a ƙasar Rasha.

Italiya da kuma Brazil ne kaɗai a tarihin hasar cin kofin duniya suka taba kafa wannan tarihin na ɗaukar Kofin sau 2 a jere.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: