Wednesday, May 29, 2024

2023: Matar Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP Ta Tafka Baranbarama a Sabon Bidiyo

Manyan Labarai

Mai ɗakin ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, watau Titi Abubakar ta buga babbar baranbaramar subutar baki a bainar jama’a.

A wani bidio da ya ja hankalin da yawan ‘yan Najeriya a kafafem sada zumunta, Titi ta roki ‘yan Najeriya su zabe jam’iyyar APC maimakon jam’iyyar PDP da mijinta ke neman takara.

Yayin da take sukar jam’iyyar mai mulki bisa gaza cika wa ‘yan Najeriya alƙawurran da ta ɗaukar masu kafin hawa kan madafun iko, Titi ta yi subutar baki a fili, lamarin da ya girgiza intanet.

Matar tsohon mataimakin shugaban kasa ta tafka wannan kuskure ne yayin da ta roki ‘yan Najeriya su zaɓi APC a zaben shugaban kasa mai zuwa a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023.

A jawabinta, Titi Atiku Abubakar ta ce:

“Nan da ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 (ranar zaben shugaban ƙasa) kowa ya fito, duk wanda ya san har yau Katin zaɓensa watau PVC bai shiga hannunsa ba to ya je ya karbo cikin hanzari. Ya kamata mu zabi jam’iyyar APC.”

“APC mai mulki da ɗauki alkawurran aiwatar mana da abubauwa da dama a ƙasar nan amma ku kalli halin da a yau muka tsinci kan mu a ciki.”

Sai dai da yake maida martani kan wannan abu, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC, (PCC), Festus Keyamo, ya yi kokarin kare matar Atiku.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, Keyamo yace daga jin wannan magana kasan kuccewar harshe ne.

Ya ce:

“Matar Atiku, Titi Abubakar ba da jimawan nan ba ta roki mazauna Najeriya su kaɗa wa jam’iyyar APC kuri’unsu a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 na shekara mai zuwa.”

“Zancen gaskiya dai wannan kuccewar harshe ne Amma mu a wurin mu ba zamu wulakantata ba kasancewarta mace musamman idan ta yi gaggawa da gyara kuskuren da ta tafka.”

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da yan siyasa ke furta abinda ba shi ya dace su faɗa ba, a kwanakin baya Jos Atiku ya buga ta shi baranbaramar.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: