Thursday, May 30, 2024

Na Kawo Canji, Na Yi Bakin Kokarina a Matsayin Shugaba, Inji Buhari

Manyan Labarai

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yace ya yi iyakacin bakin kokarinsa ga Najeriya a zangon mulkinsa guda biyu.

Shugaban ya yi wannan furucin ne a birnin Washington DC lokacin da yake jawabin maraba ga shugaban ƙungiyar Abu Dhabi, Sheikh Al-Mahfoudh Bin Bayyah, da mataimakinsa, Fasto Bob Robert na kasar Amurka, waɗanda suka ziyarce shi.

“Muna da girma da tarin al’umma a Najeriya, ga matsaloli ta ko wane ɓangare, amma a ɓangarori da dama, mun kokarta. A tsawon shekaru Bakwai da rabi na yi iya kokarina,” inji Buhari.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya fitar, an ji Buhari na cewa warware matsalolin da suka addabi matasa gwamnatinsa ta sa a gaba saboda sune manyan gobe.

KARANTA WANNAN: 2023: Ku zabi mahaifina, yar Atiku ta roki matasa da daliban Najeriya

Buhari, wanda ya tabo bukatar gina rayuwar matasa domin kaucewa tsattsauran ra’ayin addini, ya roki kungiyar da kar ta gajiya ta ci gaba da taimaka wa rayuwar matasa, waɗanda sune shugabannin gobe.

Shugaba Buhari ya ƙara da cewa:

“Aikin da kuke yi yana da matukar amfani kuma yana taimaka wa matuƙa gaya, musamman game da matasa, su fahimci juna kuma su riƙa alfahari da al’adunsu da asalinsu.”

“Wannan babban yunkurin na ku zai taimakawa manyan gobe su yi kyakkyawan shiri kuma su zauna lafiya da aminci. A ɓangarenmu, zamu cigaba da warware kalubalen da suka zame mana karfen ƙafa, musamman waɗanda suka shafi matasa.”

Dalilin da yasa muka kawo maka ziyara – Bin Bayyah

Da yake nasa jawabin, Bin Bayyah yace sun kawo wannan ziyarar ne domin sanar da shugaban kasa Buhari kuma su gayyace shi zuwa wurin bikin karramawar da za’a masa da lambar yabon Abu Dhabi Foundation Award.

DUBA WANNAN: 2023: Atiku Da Tinubu Na Musayar Maganganu Kan Dukiya Da Mulki

Yace sun zaɓi su ba shi wannan lambar yabo ne saboda gagarumar rawar da yake takawa gagara misali wajen inganta zaman lafiya da tsaro.

Bin Bayyah ya ƙara da cewa wannna karramawa ta yi dai-dai da aikin gidauniyar na yaƙi da tsattsauran ra’ayin Addini da kuma inganta zaman lafiya da mutunta juna tsakanin addinai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya zuyarci kasar Amurka ne domin halartar taron shugabannin Afirka.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: