Wednesday, May 29, 2024

Kudin Makamai: Kotu Ta Tura Tsohon Hadimin Jonathan Gidan Kurkuku

Manyan Labarai

Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta kama tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin hulɗa da jama’a, Doyin Okupe da laifin karkatar da wasu kuɗin makamai daga Ofishin babban mai ba da shawara kan tsaro.

Alkalin Kotun mai shari’a Ijeoma Ojukwu a ranar Litinin ta yanke cewa ta kama Okupe da hannu dumu-dumu a halatta kuɗin haram kuma ta ci shi tarar naira miliyan N13m.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Okupe ne darakta janar na kwamitin yakin neman zaben Peter Obi, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party.

A 2019 hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da shi a gaban Kuliya kan tuhume-tuhume 59 da suka kunshi halasta kuɗin haram, karkatar da kuɗin makamai da suka kai miliyan N240m daga Ofishin NSA, Sambo Dasuki.

EFCC ta gurfanar da jigon siyasan ne tare da wasu kamfanoni guda biyu waɗanda suka haɗa da, Value Trust Investment Ltd da kuma Abrahams Telecoms Ltd.

Mai shari’a Ojukwu ta kama tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Jonathan da hannu da aikata laifuka 26 cikin 56 da ake tuhumarsa.

Wane hukunci Kotun ta yanke masa?

Daga nan sai Alƙalin Kotun ta yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru biyu kan kowace tuhuma ɗaya ko kuma ya biya tarar N500,000 kan kowane laifi.

Daɗin daɗawa Alkalin ta umarci cewa idan karfe 4:30 ma yammacin Litinin ta yi ba’a biya tarar ba, jami’ai su iza keyar Okupe zuwa Kurkuku.

Mai shari’a Ojukwu tace ta yanke wannan hukunci ne bayan rokon da fitattun yan Najeriya suka mata ciki har da gwamnan Anambra, Charles Soludo, daraktan hukumar NOA, Alhaji Idi Faruk, matar wanda ake zargi da ɗansa.

Alƙalin tace wanna shi ne na farko da aka kama shi da laifi kuma ba shi da tabon aikata manyan laifuka a baya, inda ta ƙara da cewa, “Ya ba da haɗin kai bai ɓata wa Kotu lokaci ba.”

A wani labarin kuma Kotun Daukaka Kara Ta Ba Uba Sani Nasara, Ta Yi Fatali Da Karar Sha’aban

Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a inuwar APC kuma Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani, ya sake samun nasara a Kotun ɗaukaka kara.

Ta yi fatali da ƙarar da sha’aban ya shigar gabanta. Tace ƙarar ta saba doka kuma babu wasu gamsassun bayanai.

Duba nan: