Monday, November 11, 2024

Yara 102: A Karshe, Manomi Mai Jikoki 568 Ya Yanke Shawarar Daina Haifan Yara

Manyan Labarai

Lusaka, Uganda – Wani manomi dan kasar Uganda, Musa Hasahya wanda ke da mata 12 da yaya 102 – tare da jikoki 568 – daga karshe ya yanke shawarar dena haihuwan yara baki daya.

Musa Hasahya, dan shekara 67, yanzu ya umurci matansa su fara kayyade iyalai, don su iya samun kudin siyan abinci da kula da iyalansa masu yawa.

 

Magidanci mai jikoki 568
Musa Hashaya, magidanci mai yaya 102 da jikoki 568

Ya fada wa The Sun, a wata hira, cewa kudin da ya ke samu na raguwa cikin yan shekarun nan saboda tsadar rayuwa kuma iyalinsa na kara yawa.

Da ya ke magana kan aure mata da yawa, ya ce:

“Na rika auren mace daya bayan daya. Ta yaya namiji zai gamsu da mace daya?”

Auren mace fiye da daya halas ne a nan – Musa Hasahya

Mr Hasahya da iyalansa da ke zaune a Lusaka, Uganda, inda galibi ana auren mata fiye da daya.

Ya yi ikirarin cewa dukkan matansa a gida daya suke zaune saboda ya rika sa ido a kansu kada su rika harka da wasu mazajen.

Ya ce:

“Dukkan mata na a gida daya suke zaune. Hakan ya fi min saukin sa ido a kansu tare da hana su tsere wa da wasu mazan a kauyen.”

KU KARANTA: An gurfanar da matar aure saboda antayawa wata mata da ke bin mijinta bashi ruwan zafi

Na dena haihuwan yara, in ji amaryar Mr Hasahya

Zulaika, matarsa mafi karancin shekaru kuma mahaifiyar yaya 11, ta sanar da cewa ba za ta sake iya haihuwan yara ba saboda tsadar rayuwa a yanzu.

A kalamanta, ta ce:

“Ba zan sake haihuwan yara ba. Na ga tsadar rayuwa kuma yanzu na fara shan maganin kayyade iyali.”

Hasahya na aiki da iyalansa a gona

Hasahya yana zaune tare da kimanin kashi uku na yayansa da shekarunsu ya kama daga shida zuwa 51 a gonarsa.

Babban dansa ya girmi matarsa mafi karancin shekaru da shekara 21, Daily Mail ta tattaro.

Saboda rashin lafiya, ba ya iya aiki yanzu, kuma biyu cikin matansa sun rabu da shi saboda rashin kudi da zai kula da su.

An Bankado Wasikar Soyayya Da Wata Budurwa Ta Aikewa Dan SS1, Jama’a Sun Yi Cece-kuce

A wani rahoton, masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga wasikar soyayya da wata yarinya ta rubutawa matashi dan aji hudu a Sakandare mai suna Somto.

Yayar yaron ta wallafa wasikar a TikTok yayin da take ja masa kunne kan harkokin makarantarsa.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: