Friday, May 31, 2024

Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Kogi, Yahaya Bello Ya Ba Ma’aikata Hutu

Manyan Labarai

Gwamnatin Jihar Kogi dake arewa ta tsakiya a Najeriya ta ba da hutun ranar Alhamis 29 ga watan Disamban, 2022 ga ma’aikatan jihar saboda karban bakuncin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaba Buhari zai ziyarci jihar Kogi ne domin kaddamar da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa da gwamna Yahaya Bello ya kammala domin inganta rayuwar al’umma.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin sadarwa, Kingsley Fanwo, ya raba wa manema labarai ranar Lahadi a Lokoja, babban birnin Kogi.

Gwamnatin Kogi karkashin jagorancin Yahaya Bello ta roki mazauna jihar da su baiwa maraɗa kunya su fito kwansu da kwarkwata su yi maraba da shugaban ƙasa ranar Alhamis.

Haka zalika gwamnatin ta bukaci ɗaukacin al’umma su nuna wa duniya karamcin da aka sansu da shi yayin da mai girma shugaban ƙasa zai zo jiharsu kuma a kan abinda ya shafe su.

Sanarwan da kwamishinan ya fitar ta ce:

“Shugaban kasa kuma kwamandan Dakarun tsaro a Najeriya, Muhammadu Buhari, zai zo mana ziyara ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba, 20222 domin buɗe wasu muhimman ayyukan raya kasa.”

“Bisa haka da kuma tabbatar da komai ya tafi daidai yayin maraba da shugaban ƙasa, gwamnatin jahar Kogi karkashin shugabancin gwamna Yahaya Bello na farin cikrin sanar da cewa ta bayar da hutun ranar Alhamis, 29 ga watan Nuwamba, 2022.”

Bugu da kari, gwamnatin Kogi ta roki kungiyoyin ma’aikata da hukumomin tsaro su tabbatar da abin doka cikin zaman lafiya da kwanciyar hankula yayin ziyarorin shugaban ƙasa Buhari a wannan rana.

A wani labarin kuma Gwamna Ribas Nyeson Wike ya sha alwashin bayyana ɗan takarar shugaban kasan da zai goyi baya a 2023

Yayin da yake jawabi a wurin kaddamar da gadar sama ta 10 da gwamnatinsa ta gina a ƙaramar hukumar Abio-Akpor, jihar Ribas, gwamna Wike yace jira ya ƙare.

Gwamna Wike jagoran tafiyar G-5 da ta kunshi gwamnonin PDP biyar da wasu jiga-jigai na takun saka da shugabancin jam’iyya na kasa bayan nasarar Atiku a zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa.

Duba nan: