Friday, May 31, 2024

An gurfanar da matar aure saboda antayawa wata mata da ke bin mijinta bashi ruwan zafi

Manyan Labarai

Kenya – An gurfanar da wata mata a kotu a Kenya saboda antayawa wata mata da ke bin mijinta bashin kudi ruwan zafi, ta kuma mata rauni.

Cecilia Kingi Muuo ta musanta aikata laifin yayin da aka gurfanar da ita gaban alkalin kotun Mombasa, Vincent Adet, rahoton LIB.

Wacce ake zargi
Matar da ake zargin da zuba wa wata ruwan zafi saboda ta zo karbar bashi hannun mijinta. Hoto: LIB

 

Wacce abin ya faru da ita mai suna Faith Chelangat, ta tafi gidan Muu ne domin neman a biya ta kudin da ta ke bi bashi.

Amma, wacce ake zargin ta fada mata cewa mijinta baya gida a lokacin. Sai dai, ta tarbe ta ta bukaci ta shigo cikin gida ta zauna ta jira shi.

Makwabta suka ceci matar da ta zo karbar bashi

Muuo wacce ta fara dafa ruwan zafi don girki, nan take ta rikide ta fusata ta antayawa Chelangat ruwan zafin tana gargadin ta dena bin mijinta.

KU KARANTA: Rudani A Kotu Yayin Da Wani Mutum Ya Yi Kokarin Nuna Wa Alkali Mazakutansa

Makwabta ne suka ceto wacce abin ya faru da ita sannan sua garzaya da ita zuwa asibiti.

An saki wanda ake zargin kan beli na Ksh 50,000 da mutum daya da ya tsaya mata.
Za a cigaba da shari’ar a ranar 11 ga watan Janairun 2023.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: