Kenya – An yi wani abu mai kama da dirama a kotu a ranar Litinin 19 ga watan Disamba, a yayin da wani mutum ya yi kokarin nuna wa alkali mazakutansa a yayin da ya yi ikirarin cewa yan sanda daga caji ofis din Nairobi a Kenya bayan kama shi.
An gurfanar da shi Clement Odera wanda aka fi sani da Hamisi a gaban alkalin kotun majistare na Milimani, Micheni Wendykan zarginsa da hadin baki don damfarar wani mai neman aiki, rahoton LIB.
An zargi cewa tsakanin 1 ga watan Nuwamban 2021, da ranar 25 ga watan Oktoban 2022, ya hada baki da wani mutum ba a riga an kama ba don damfarar wani Christopher Nyalenda Sino kudi Ksh 1,866 da sunan za su nema masa aikin direba na kwamishinan harkokin shari’a (JSC).
Amma, yayin zaman kotu a ranar Litinin, Odera ya yi kokarin tube wandonsa a yayin da ya ke fada wa alkali cewa gabansa ya kumbura saboda rauni da ya yi yayin dukansa da yan sanda suka yi don tilasta masa amsa laifin.
Ya ce:
“Yan sanda sun min duka. Idan na nuna maka gaba na, ya kumbura. Sun lakada min duka kuma suka ce in amince da laifin.”
DUBA WANNAN:Â Abduljabbar Kabara: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Malamin Kano Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa
Matakin da alkali ya dauka
Biyo bayan wannan ikirarin, alkalin kotun ya bada umurnin a cigaba da tsare wanda ake tuhumar a caji ofis.
Wendy ta kuma umurci dan sandan da ke kula da caji ofis din ya kai wanda ake zargin asibiti don a duba shi.
Kotun ta kuma bukaci jami’in dan sandan ya dawo wa kotu sakamakon rahoton likita.
Daga bisani an saki Odera bayan ya biya belin Ksh 500,000.
Kotu ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya
A wani rahoton, kun ji cewa kotun shari’a da ke jihar Kano ta yanke hukuncin kisa malamin addinin musulunci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara bayan samunsa da laifin batanci ga Annabi (SAW).
Tunda farko, gwamnatin jihar Kaduna ta shirya mukabula tsakanin Abduljabbar da wasu malamai na jihar Kano daga kungiyoyi daban-daban don bashi damar kare kansa daga zargin.
Tushe: News Brief Hausa