Wasu matasa 19 sun shiga hannun Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, kan kokarin hada auren jinsi daya a jihar.
Wadanda aka kaman, wadanda mafi yawansu mata ne sun yi kokarin daura wa wasu maza biyu masu suna Abba da Mujahid aure a matsayin mata da miji.
Kakakin hukumar ta Hisbah, Lawan Ibrahim ya tabbatar da kama matasan a ranar Talata, 20 ga watan Disamba, Daily Nigerian ta rahoto.
Kamar yadda ya bayyana, jamiāan hukumar sun yi wa wajen da za a daura auren dirar mikiya, inda suka damke mata 15 da wasu maza hudu.
Sai dai kuma wadanda ake shirin daurawa auren wato ango da amarya (Abba da Mujahid) sun arce bayan da suka ga isowar yan hisban.
Ibrahim ya ce:
“An kama mutanen ne bayan wani mutum ya sanar da hukumar shirin da wasu ke yi na kulla auren jinsi daya.
“Jami’anmu da ke aiki da hedkwatar hukumar Hisbah ta Sharada Kano, sun yi wa wajen dirar mikiya kafin a daura aure.
“Daga cikin wadanda aka kama akwai mata 15 da maza hudu. “
“Abba da Mujahid sun gudu a lokacin da suka hango zuwan jami’an Hisbah wajen daurin auren, amma wacce ta shirya bikin, Salma Usman mai shekaru 21 na a hannunmu.
“Za a mika wadanda aka kama zuwa ga yan sanda don daukar matakin da ya kamata kasancewar yawancinsu matan sun yi ikirarin cewa an gayyace su zuwa daurin auren ne daga jihohin da ke makwabtaka. Za mu tabbatar da ganin cewa an kama Abba da Mujahid.āĀ
Hakazalika Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Haruna Ibn Sina, ya ce Ā tuni hukumar ta kaddamar da bincike don gurfanar da wadanda suka shiga hannunta, wanda a cewar wasu daga cikinsu gayyatarsu aka yi zuwa wajen daurin auren.
Sai dai kuma, ya ce wasu daga cikin wadanda aka kama din sun roki da a yi musu sassauci bisa sharadin ba za su sake aikata laifin ba.
A wani labari na daban, an yi wani abu mai kama da dirama a kotu a ranar Litinin 19 ga watan Disamba, a yayin da wani mutum ya yi kokarin nuna wa alkali mazakutansa a yayin da ya yi ikirarin cewa yan sanda daga caji ofis din Nairobi a Kenya bayan kama shi.
An gurfanar da shi Clement Odera wanda aka fi sani da Hamisi a gaban alkalin kotun majistare na Milimani, Micheni Wendykan zarginsa da hadin baki don damfarar wani mai neman aiki.