Saturday, June 1, 2024

Yanzun nan: Kotu ta Yanke Hukuncin a Rataye Sheikh Abduljabbar Kabara

Manyan Labarai

Kotu ta yankewa Abduljabbar Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Akali ya yanke hukunci da cewa:

A cewar Alkali: Sashi na ɗati uku da sittin da uku sashin (f) ya bada hukunci haka:

“Anyekewa Abduljabar hukuncin kisa Ta hanyar rataya.

“Saahi 380 ne ya bada wannan hukuncin ta hanyar rataya.

“Kuma kotu ta kwace litttafansa da ya gabatar da su a gaban kotu dan sheda.

“Kuma kotu ta bada umarnin kwace masallatansa gudu biyu Na filin Mushe dana Unguwar sabuwar Gwandu”

Abduljabbar ya ce ba da yawunsa aka nema masa sassauci ba

A kalamansa:

“Ni bana neman sassauci akan laifin da ban yi ba, ina bawa masoyana hakuri, kar su samu damuwa kan tafiya ta lahira, zanyi mutuwa ta girma, kuma bana neman kai Ibrahim Sarki kayi mun sassauci, kuma a gaggauta yi mun hukuncin Kalami na na karshe kenan.”

Abduljabbar a Kotun Kano
Abduljabbar Nasiru Kabara. Hoto: Daily Trust

Shinfida:

  • A yau ne alkali zai yanke hukuncin kan karar da aka shigar kan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda ake zargi da yiwa Annabin Rahama SAW batanci a cikin karatuttukansa da dama.
  • Tuni dai Abduljabbar da mukarrabansa; lauyoyi da sauran jama’a suka hallara a kotu don jin abin da alkali zai yanke.
  • Jami’an tsaro sun taru domin tabbatar da an yi shari’ar cikin aminci, kamar yadda wakilinmu a jihar Kani ya aiko mana.
  • Bayan sauraran hujjoji, alkali ya ce tabbas ya kama Abduljabbar da laifin batanci ga ma’aiki SAW.
  • Alkalin ya ce, bisa hujjojin da ya samu, Abduljabbar ne ya kirkiri dukkan maganganun batanci ya jingina ma Annabi SAW, don haka zai hukunta shi.

Ku bibiye mu domin karin haske da cikakkun rahotanni kan yadda shari’ar ke tafiya…

DUBA NAN: Zagin Annabi: An tsaurara tsaro yayin da kotu za ta yanke hukunci kan Abduljabbar a yau

Duba nan: