Saturday, November 9, 2024

Mambobin APC Sama da 10,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Wurin Gangamin Atiku Na Nasarawa

Manyan Labarai

Jam’iyyar PDP ta samu gagarumin ƙarin goyon baya a ɗaya daga cikin jihohin da jam’iyyar APC ke mulki a arewacin Najeriya.

Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya karbi tuban mambobin APC akalla 10,000 waɗanda suka gaji da tsintsiya suka rungumi laima a jihar Nasarawa.

Da yake maraba da dubbannin masu sauya shekar, Atiku tare da shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya yaba musu bisa kwarin guiwar da suka samu na tattara komatsansu daga APC.

Yace jam’iyyar APC a matakin ƙasa da jihohi da gaza ɗanɗanawa al’umma romon demokaraɗiyya tun farkon mulkinta har zuwa yanzu inda ya kara da cewa zai gyara baki ɗaya kuskuren idan ya zama shugaban ƙasa a 2023.

Daɗin daɗawa ya yi alkawarin samar da ayyukan yi ga matasa a sassan kananan hukumomi 13 na jihar kana zai aiwatar da muhimman ayyuka don ta da komaɗar tattalin arziki.

Jaridar Punch ta rahoto Tsohon mataimakin shugaban kasan na cewa:

Idan aka zabe ni na zama shugaban kasa a 2023 zan ware Dala biliyan $10bn domin samar da ayyukan yi ga matasa da mata.”

“Ina mai muku albishir da cewa gwamnati na zata gwangwaje ku da Titunan da zasu haɗa Nasarawa da sauran jihohin da suke makwaftaka da ku.”

“Saboda haka abinda muke son da ku su dangwala mana kuri’unku a zabe mai zuwa kamar yadda kuka nuna mana a ana tare a zabukan da suka gabata.”

A nasa ɓangaren, shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu duk da jam’iyyar PDP ke jan ragamar Nasarawa yana da kwarin guiwar Atiku zai lashe kaso 95 cikin ɗari na kuri’un mazauna jihar.

Mutane sun nuna suna tare da ‘yan takarar PDP – David Ombugadu

Tun a jawabin maraba, mai neman zama gwamnan Nasarawa a inuwar PDP, David Ombugadu, yace bisa la’akari da cikar mutane a wurin gangamin, ya nuna alamun aniyarsu ta zaɓen ‘yan takarar PDP tun daga sama har ƙasa a 2023.

Ya kara da cewa daga lokacin da ya sa hannu a siyasa a 2011 zuwa yanzun ya samar da ingantacciyar kula da lafiya ga mutane sama da 18,000 a Nasarawa.

Yace:

“Ina kalubalantar mutane su tabbata jam’iyyar PDP ta ɗare madafun iko a 2023. Lokaci ya yi da mutane zasu warke daga ciwan yunwa, talauci da matsin rayuwa karkashin gwamnatin APC.”

 

Duba nan: