Wednesday, May 29, 2024

2023: Bola Tinubu Ya Dira Birnin Kaduna Tare da Jiga-Jigan Jam’iyyar APC

Manyan Labarai

Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya dira birnin Kadunahttps://thenationonlineng.net/tinubu-arrives-kaduna-for-presidential-campaign gabanin kaddamar da fara kamfe a arewa maso yamma.

The Nation ta tattaro cewa Tinubu, wanda ya biyo jirgin Kanam Air, ya samu kayyawar tarba a Air Force Base daga gwamna Malam El-Rufai, Uba Sani, ɗan takarar gwamnan Kaduna, shugaban majalisar dokoki da sauran kusoshin gwmnati.

Jirgin Tinubu ya sauka a Kaduna da misalin karfe 2:30 na rana tare da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Abubakar Badaru na Jigawa da Simon Lalong na jihar Filato.

DUBA WANNAN: Na Kawo Canji, Na Yi Bakin Kokarina a Matsayin Shugaba, Inji Buhari

Haka zalika News Brief Hausa ta fahimci cewa abokin gamin Tinubu kuma tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima, ya isa Kaduna a wani jirgin na daban tare da tawagarsa.

Ana tsammanin Bola Tinubu zai gana ɗa masu ruwa da tsaki da suka haɗa da ‘yan kasuwa, shugabannin addinai da Sarakunan gargajiya a ranar Litininn da daddare.

Bugu da kari. An tsara gudanar da gamgamin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a babban Filin wasan Ahmadu Bello ranar Talata.

Ana zaton miliyoyin magoya bayan jam’iyyar APC a lungu da sakon shiyyar arewa maso yammacin Najeriya zasu yi tururuwa zuwa wurin gangamin domin nuna goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Legas.

DUBA WANNAN: Mambobin Jam’iyyar PDP Sun Sauya Sheka Zuwa NNPP A Gombe

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Tinubu ya dawo daga birnin Landan inda ya yi jawabi a Catham House kana ya yi hira da BBC.

Idan baku manta ba, APC ta kaddamar da fara yakin neman zaɓen shugaban kasa ne a Jos, babban birnin jihar Filato, jihar daraktan kamfen na ƙasa, Simon Lalong.

Duba nan: