Wednesday, May 29, 2024

2023: Ba Zan Goyi Bayan Atiku Ba, Ina Tare da Obi, Babachir Lawal

Manyan Labarai

Tsohon SGF, Babachir Lawal, ya musanta raɗe-raɗin dake yawo cewa ya jingine Peter Obi, ya koma bayan ɗan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Tsohon Sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal, ranar Litinin, ya jaddada cewa ba zai goyi bayan ɗan takarar ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar ba a zaɓen 2023, rahoton Punch.

A cewarsa burin Atiku bai yi dai-dai da tsarin da ya dace na sauya gwamnati ba domin zai kasance daga shugaban ƙasa bafullatanin Musulmi zuwa wani shugaban Bafullatani kuma Musulmi.

Lawal ya yi wannan karin hasken ne yayin da yake martani kan rahoton da ya karaɗe soshiyal midiya cewa ya jingini ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi, ya koma gidan Atiku.

DUBA WANNAN: Mambobin Jam’iyyar PDP Sun Sauya Sheka Zuwa NNPP A Gombe

Ya gargaɗi cewa idan har Atiku ya kai ga nasara alama ce dake nuna ƙabila ɗaya ta mamaye sauran, kamar yadda rahoton Punch ya tabbatar.

A wata sanarwa da Lawal ya fitar ya jaddada goyon bayansa ga mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar LP, Peter Obi, inda yace, “Ina nan a matsayin ɗan amutun Obi.”

Tsohon SGF yace:

“Yanzu nake gani wani labari na yawo cewa na bar tafiyar Peter Obi na koma aiki da Atiku Abubakar. Babu ƙansin gaskiya a wannan zance, ban taba ko da tunani ko tantamar shiga PDP ba domin ina kallon jam’iyyar a matsayin mafi muni da ta haɗa yan kanzagi da masu kwaɗayin mulki don kansu.”

“Baya ga haka ma, na tsinci kaina a wata shekara da na sha fama da faɗi tashin takaddama da Fulani waɗanda ke tura dabbobinsu su shiga cikin gonata su cinye mun amfani kusan duk shekara.”

DUBA WANNAN: Daruruwan Mambobin PDP da Jiga-Jigai Sun Koma APC a Katsina

“Wannan matsalar ba ni kaɗai bane, haka suke wa dattawan mu da sauran manoma a sassan arewacin Najeriya. Duk suna haka ne su ɓata mana amfanin gon saboda ƙeta kuma abin mamaki shugabanninsu dake cikin gwamnati sun kama bakinsu sun yi shiru.”

“Bugu da ƙari, ni ina ganin sauya gwamnati daga Fulani Musulmi zuwa wani Fulani Musulmi ya fi muni fiye da takarar Musulmi da Musulmi. Yana wakiltar Kabila ɗaya ta mamaye komai, ta latse sauran kabilu.”

“Ina nan a matsayin ɗan a mutun Peter Obi, dum wani labari da ba haka ba karya ne.”

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: