Masu iya magana kan ce soyayya babu ruwanta da kudi, sura ko kuma kyau. Da zaran zukata biyu sun hadu basa ganin kowa da komai sai junansu.
Hakan ce ta kasance a bangaren wasu ma’aurata wadanda ko kusa basu yi kamanceceniya ta wajen sura ba.
Yayin da angon ya kasance dogo mai ji da tsaye lamba daya, matar ta kasance yar tsirit gajeruwa a kasa. Sai dai hakan bai hana su shuakin junansu ba.
Jama’a sun yi cece-kuce a soshiyal midiya bayan bayyanar hotunan ma’auratan inda suka matukar dauka hankali da birgesu.
Mutumin mai suna Thabelo Madiba ya garzaya manhajar Twitter domin nunawa duniya sahibarsa da yaransu dauke da taken “muna shan soyayya a nan bangaren.”
Matashin mai shekaru 27 ya kai tsawon mita 2.6. Hotunan ma’auratan ya shahara sosai a dandalin sada zumuntar, inda ya samu martani da dama.
Mutane da dama sun yi ba’a a kan hotunan.
Jama’a sun yi martani
@PapaJ_Sono ya ce:
“Wasu ma’auratan tsayinsu daya, amma basa nuna mana irin soyayyar da ku kuke nuna mana. Allah ya yi maku albarka, kuna karfafa mana gwiwa.”
@Tsoro02 ta ce:
“Magana ta gaskiya ma’auratan nan sun shafe shekaru suna soyayya, ina taya ku murna da kuka karfafa abun kuma kun samu albarkar haihuwar da ma.”
@_missygirl00 ta ce:
“Yaya kuka yi abin…yawanci soyayya da masu tsawo baya aiki.”
@Normanbooz ta ce:
“Ba za ta iya ganinsa ba idan yana kallon sauran yan mata yayin da yake tare da ita.”
Karamar yarinya ta bukaci a daura aurenta da mahaifinta
A wani labarin kuma, wata karamar yarinya ta bar mutane baki bude a soshiyal midiya bayan ta bukaci a daura mata aure da mahaifinta.
Yarinyar wacce ta ci ado sanye da doguwar riga irin na amare inda ta bukaci ayi abun da ya kamata na daura aren ba tare da bata lokaci ba. Wannan batu ya baiwa mutane dariya da mamaki inda wasu ke cewa tana son yiwa mahaifiyarta karan tsaye.
Wayon yarinyar ya matukar daukar hankalin jama’a inda suka tofa albarkacin bakunansu tare da cewa lallai da ganin mahaifin nata na kula da mamanta sosai shiyasa ita ma take so ta rabe.