Monday, June 3, 2024

An Kama Wani Mutum Mai Shekaru 49 Yana Wanka da Jini a Ogun

Manyan Labarai

Jihar Ogun – ‘Yan sanda a jihar Ogun sun cafke wani mutum mai suna Ganiyu Shina dan shekara 49 da haihuwa, bisa zarginsa da yin wanka da jini a gabar kogi a jihar Ogun.

Shina, wanda ke zaune a karamar hukumar Odeda, an kama shi ne a yau Alhamis a wani kogi a Kotopo, rahoton Daily Trust.

An kama wanda ake zargin ne a lokacin da jama’ar unguwar suka gan shi a bakin kogi, inda aka ga ya ajiye abun hawansa ya fito dauke da soso da wani kwantena cike da jini ya fara wanka da shi.

KARANTA WANNAN: Tarihin Masarautun Arewa: Jerin Manyan Sarakuna 10 na Arewacin Najeriya

Yadda aka kama mutumin yana wanka da jini

Abimbola Oyeyemi, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma bayyana cewa:

“Yana tsaka da wankan sai ya fahimci ana kallon sa , inda ya ranta ana kare sai dai ‘yan unguwar sun yi nasarar cafke shi.”

Ya ce a lokacin da ‘yan sandan suka sami labarin abunda ke faruwa a hedikwatar sashen Aregbe ta hannun wani dan unguwar, jami’in ‘yan sanda na sashen, Bunmi Asogbon sun yi gaggawar jagorantar tawagar ‘yan sintiri zuwa wurin, inda aka kamo wanda ake zargin zuwa ofishin.

KARANTA WANNAN: Fasahar zamani: Yadda kasar Jamus ta kirkiro injin kyankyasar jarirai

Oyeyemi ya bayyana cewa, a yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya ce bokan sa ne ya basa sirrin aikata hakan.

Da jinin me yake wanka, ya yi bayani

Wanda ake zargin ya ce jinin da ya yi amfani da shi na saniya ne ba na mutun ba ne.

“A lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa yana da matsala ta rashin lafiya kuma wani likitan gargajia ya umarce shi da ya yi hakan.

“Ya kara da cewa jinin da yayi amfani da shi ba jinin mutum ba ne, na saniya ne,” in ji shi.

Oyeyemi ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a dauki sauran jinin domin bincike a dakin gwaje-gwaje domin sanin ko da da gaske ba jinin mutum ba ne.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: