Thursday, August 31, 2023

Rikici a Gidan Kwankwaso, Dan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus

Manyan Labarai

Niger – Ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar Neja a inuwar jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, John Bahago, ya janye daga takara kana ya fice daga jam’iyyar.

Mista Bahago, tsohon mamba a majalisar dokokin jihar, ya sanar da haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban NNPP a gundumar Guni mai kwanan watan 14 ga Disamba, 2022.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa ya tura kwafin wasiƙar zuwa ga shugaban jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Munya da kuma shugaban jiha da na ƙasa.
A cikin takardar, Mista Bahago ya gode wa jam’iyyar bisa ganin ya dace da zama abokin takatar mai neman zama gwamna a inuwar NNPP, Yahaya Ibrahim-Sokodeke.
Wasiƙar Mista Bahago ta ce:
“Ni, John Paul Bahago, daga gundumar Guni yankin Munya, mai lambar zama mamba 003, na yi murabus daga matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna ga Alhaji Yahaya Ibrahim Mohammed, a inuwar NNPP.”
“Haka nan kuma na fita daga jam’iyyar NNPP, ina godiya bisa zaɓo ni da kuma goya mun baya na zama ɗan takarar mataimakin gwamna.”
Duk da bai faɗi makasudin ɗaukar wannan mataki ba amma wasu bayanai sun nuna cewa an fara zaman doya da manja tsakanin NNPP reshen Neja da Mista Sokodeke, ɗan takarar gwamna.
A watan Yuli, kwamitin ayyuka na NNPP ta jihar Neja ya kai ƙorafi ga uwar jam’iyya ta ƙasa inda ya nemi mahukunta a jam’iyyar su rushe zaben fidda gwanin da ya samar da Alhaji Yahaya Ibrahim Mohammed a matsayin ɗan takarar gwamna.
Bayan haka jam’iyyar ta shirya wani sabon zabe mai cike da ruɗani wanda ya ayyana tsohon ɗan takarar gwamna a Inuwar APC, Idris Malagi a matsayin ɗan takarar NNPP.
Amma Mista Malagi, wanda har yau yake mamban jam’iyyar APC, ya fito fili ya nesanta kansa daga zama ɗan takarar gwamnan NNPP.
Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: