Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa yan Arewa ba su da wani dalili da zai hana su zabar dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A cewarsa, Tinubu ya yi sadaukarwa mai tarin yawa wajen bunkasa Dimokradiyya da ci gaban Najeriya, musamman a kokarinsa na goyon bayan dan Arewa ya zama Shugaban Kasa don haka lokacin ramawa kura aniyarta ya yi, Daily Trust ta rahoto.
Ganduje ya yi martanin ne yayin wani taro da wata kungiya mai suna Volunteers for Democracy, karkashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji ta shirya a Kano a ranar Asabar.
Ganduje ya ce:
“Arewa da yan arewa ba su da wani dalili na kin goyon bayan Tinubu da zabar jam’iyyar APC. Bola Ahmed Tinubu ya taka rawar gani sosai kuma ya taimakawa yan arewa da cigaban Najeriya. Don haka, lokacin ramawa kura amiyarta ya yi.
“Tinubu ya goya wa Shugaba Buhari baya har sai da ya zama shugaban kasa. Bai nemi a bashi kowani mukamin siyasa ba kuma ya cigaba da goyon bayan gwamnati. Ban taba ganin mai kaunar arewa kamar shi ba.”
Daga Karshe, Obasanjo Ya Mara Wa Peter Obi Baya, Ya Bayyana Dalili
A wani labarin, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya fito fili ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, gabanin zaben shugaban kasa na Fabrairun 2023.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a sakonsa na sabon shekara mai taken ‘kira ta ga yan Najeriya musamman matasa.’
Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa babu waliyyi cikin yan takarar shugaban kasar, amma idan ana batun ilimi, ladabtawar da abin da za su iya yi, Obi na gaba da sauran.
Obasanjo, cikin sakon da ya rattaba hannunsa ya ce:
“Babu waliyyi cikin yan takarar amma idan aka kwatanta abin da suka yi a baya, fahimtarsu, ilimi, da lafiya da abin da za su iya yi musamman duba da inda kasar ta tsinci kanta yau da kwarewata kan aikin da nima na yi, Peter Obi, wanda na ke matsayin mai koyarwa a wurinsa shine ke kan gaba.
“Sauran kamar sauran mu suna da rawar da za su taka don ceto Najeriya. Wani abu mai muhimmanci game da Peter shine tamkar allura ya ke da ya hada arewa da kudu kuma ba zai bata ba.”