Friday, May 31, 2024

Jigon APC Kuma Surukin Ministan Buhari Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

Manyan Labarai

Wani babban jigon jam’iyyar APC a jihar Sakkwato kuma dan surukin Ministan Ministan harkokin ‘yan sanda a gwamnatin Buhari, Muhammad Dingyadi, ya sauya sheka zuwa PDP.

Zayyanu Wamakko wanda ya kasancen ɗan surukin Ministan yan sanda, Muhammad Dingyadi ya tabbatar da ficewarsa daga APC zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a Sakkwato.

Jaridar PM News ta tattaro cewa baya ga haka, Zayyanu, ya kasancen ɗan dagi ga jagoran APC a Jahar Sakkwato kuma tsohon gwamna, Sanata Aliyu Magatakardan Wamakko.

Ya sauya sheka daga APC zuwa PDP ne a wurin gangamin yakin neman zaben da ya gudana a mahaifar tsohon gwamnan ranar Lahada a cewar sanawar da Muhammad Bello, Mai magana da yawun gwamna Aminu Tambuwal ya fitar.

Tsohon jigon APC a jihar ya shaida wa dumbin magoya bayan PDP a wurin ralin kamfen cewa ya ɗauki wannan matakin ne ganin irin tagomashin ci gaban da Aminu Tambuwal ke da shi.

Ya kara da cewa romon demokaradiyyar da ayyukan ci gaban da gwamnatin Tambuwal ya kawo wa mutanen Sakkwato ne suka ja hankalinsa tare da tawagar magoya bayansa suka yanke shigowa PDP.

Bugu da kari ya jaddada aniyarsa ta aiki ba dare ba rana tare da sabuwar jam’iyyarsa domin inganta rayuwar talakawan jahar Sakkkwato.

Ni zan lashe zabe mai zuwa – Mannir Dan Iya

Da yake nasa jawabin a wurin gangamin taron, mataimakin gwamnan Sakkwato, Mannir Muhammad Dan Iya, wanda ke kalubalantar kujerar Sanata Aliyu Wamakko a mazabar Sakkwato ta arewa, ya sha alwashin cewa shi zai ci zaben 2023 mai zuwa.

Dan Iya ya jaddada cewa kafin Karfe 12 na rana ya yi kasa-kasa da babban abokin hamayyarsa a ranar zabe.

A wani labarin kuma Gwamna Ganduje ya bayyana dalilin da yasa yan arewa ba su da zabin da wuce Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023

A cewar gwamnan na Kano, Tinubu ya yi sadaukarwa mai tarin yawa wajen bunkasa Dimokradiyya da ci gaban Najeriya, musamman a kokarinsa na goyon bayan dan Arewa ya zama Shugaban Kasa don haka lokacin ramawa kura aniyarta ya yi.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: