Abuja – Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi fatali da daukaka karar da mai neman takarar gwamna Sani Sha’aban ya shigar kan nasarar Uba Sani na APC a zaben cikin gida, rahoton Vanguard.
Mai dauko wa Legit.ng rahoto a Kaduna, Nasir Danbatta ya rahoto cewa yayin watsi da karar kotun ta ce daukaka karar ba bisa ka’ida aka yi ta ba, sannan bayanai ba su cika ba.
Sha’aban ya daukaka kara kan hukuncin Babban Kotun Tarayya da ke Kaduna da aka yanke a ranar 4 ga watan Nuwamban 2022, wacce ta yi watsi da karar kan dalilin cewa bata da hurumin sauraron karar.
Rashin gamsuwa da wannan hukuncin kotu, Sha’aban ya garzaya kotun daukaka kara.
Uba Sani da Sani Sha’aban: Lauyan APC ya tabbatar da nasarar Uba Sani
Barista Sule Shuaibu wanda shine lauyan jam’iyyar APC ya tabbatar da cewa tabbatar da hukuncin da kotun Abujan wacce ta bawa Sanata Uba Sani, dan takarar gwamna na jam’iyyar nasara.
Ya kara da cewa dukkan alkalai ukun da suka yi alkalanci sunyi tarayya a kan hukuncin da aka yanke a ranar Laraba a Abuja.
Tushe: News Brief Hausa