Thursday, May 30, 2024

Lalatattun Takardun Naira: EFCC Da Yan Sandan Benue Sunyi Karin Haske

Manyan Labarai

BenueHukumar yaki da rashawa ta EFCC da ke Makurdi, da yan sandan jihar Benue sun karyata rahoton da ke yawo a dandalin sada zumunta na cewa an gano tsaffin takardun naira a babban birnin jihar.

Bidiyon ya nuna buhunan da aka ce tsaffin lalatattun takardun naira ne a cikin babban kwantena kusa da kasuwar Wadata a ranar Talata.

Amma, jami’in hukumar yaki da rashawar wanda ya ce kada a ambaci sunansa don ba a bashi izinin magana kan lamarin ya ce ofishinsu ta samu bayani kan buhunnan tsaffin nairorin kuma suka tura jami’ansu amma aka gano lalatattun naira ne daga babban bankin kasa, CBN.

Jami’in na CBN a hirar wayar tarho a ranar Talata ya fada wa wakilin The Punch cewa:

“Wanda ya mallaki tsaffin nairarin ya ce daga CBN ya siyo. An yanka takardun nairan an kuma yamutsa su, don haka ba za a kira shi ba.

“Zan turo hotunan abin da ke cikin buhunnan domin ku gani.”

Martanin yan sandan Najeriya kan buhunnan kudi da aka gano a Benue

Abin da rundunar yan sanda ta ce game da takardun bidiyon takardun nairan
Kazalika, sanarwa da rundunar yan sanda ta fitar a daren ranar Talata ta bayyana rahoton a matsayin mara tushe.

A cewar sanarwar da kakakin yan sanda, Catherine Anene, ta fitar, abin da ake cewa naira ne takardun da ba a bukatarsu ne daga CBN.

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“A ranar 13 ga watan Disamban 2022, misalin karfe 12 na rana, mun samu rahoto a ofishin mu na Makurdi, cewa an gano naira da aka boye a barikin yan sanda na Wadata.

“Yan sanda da aka tura bincike sun gano takardu marasa kyau a wani shago kusa da barikin yan sanda da ke Wadata, Makurdi.”

Daga CBN na karbo, maganin sauro ake yi da shi – Isah Suleiman

“Mai shagon, Mr Isah Suleiman, ya gabatar da lasisin sarrafa shara da CBN ta bashi a lokacin da aka gayyace shi amsa tambayoyi.

“Ya kara da cewa an saba karbo irin wannan lalatattun takardun nairan daga CBN don sarrafa su zuwa maganin sauro. An tuntubi CBN don tabbatarwa yayin da ake cigaba da bincike.”

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: