Thursday, August 31, 2023

Bayan sun gina gidansu, ma’aurata sun tare babu kayan daki, an gano su suna bacci a kasa

Manyan Labarai

Jama’a sun yi martani bayan ganin bidiyon wasu ma’aurata suna bacci tare hankali kwance a kasa a cikin sabon gidansu.

Matar wacce ta wallafa bidiyon a dandalin TikTok ta bayyana cewa kwanan nan suka kammala ginin gidan sannan suka tare abun su a haka.

A cewarta, babu kayan daki ko daya a cikin gidan domin sai a shekara mai zuwa ne za sui so.

A cikin bidiyon, sun rufe kansu da wani dan kyallen zani yayin da suka kwanta tare a kasa. Wani wurin kuma ya nuno su zaune a kan bene yayin da suke cin kayan makulashe cikin shauki da kaunar juna.

Jama’a da dama sun karfafawa ma’auratan gwiwa, inda suka jinjina masu a kan wannan kokari da suka yi na mallakar gida sukutum.

Gidan ya birge masu amfani da dandalin TikTok saboda tsananin haduwar da ya yi gashi ginin bene irin na zamani wanda sai wane da wane ke mallakar irinsa.

Hakazalika, duba ga haduwar da gidan ya yi ya cancanci a jira duk lokacin da kayan dakin zai iso kafin a zuba domin bai dace da tsoffin kaya ba.

Ta rubuta:

“Da gaske muna bacci a kasa cikin farin ciki”

Jama’a sun yi martani

nontsikelelomolef ta ce:

“Haka ni da mijina muka fara, magana ta gaskiya shine lokaci mafi dadi a rayuwarmu.

Mapolo Mpondo ta ce:

“Ya yi kyau…Gida mai kyau kenan kuka gina…ya cancanci a jira kayan daki…ina taya ku murna da sabon gidanku.”

Brenda Fancy Abrams ta ce:

“An kammala babban aiki kuma wadannan sune yan kwaskwariman karshe da za a yin a taya ku murna da kammala sabon gidanku..ni’ima ne ki ji dadinki.”

user2459428089347 ya ce:

“Wannan ba komai bane abun da ya fi muhimmanci shine cewa kun mallaki gida mai kyau komai da ya saura zai biyo baya. Na tayaki murna da wannan sabon gida mai kyau.”

ChrisMot33 ya ce:

“Abun da ya fi shine mallakar gida naka na kanka. Na taya ki murn ni’ima a kan ni’ima.”

Matshepo Moeketsi ta ce:

“Magana ta gaskiya ita ce gaskiya gidan ya hadu! Wannan irin babban nasara haka.”

Miss Skye ta ce:

“Akalla kuna kwance a irin gidan da kuke mafarkin samu.”

Tushe: Newsbrief Hausa

Duba nan: