Jihar Kano – Babban kotun shari’a da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan malamin addinin musulunci Abduljabbar Nasiru Kabara.
Tunda farko kotun ta kama malamin da laifi bayan samun an gurfanar da shi kan zargin batanci da Annabi (SAW).
Daily Trust ta yi karin haske kan wasu abubuwa da ta yi wu ba ku sani game da malamin da ya tsinci kansa cikin rikici a yanzu.
Takaitaccen tarihin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Abduljabbar Nasiru Kabara malamin addinin musulunci ne na darikar Kadiriyya a Kano, dan shekara 52 da ake zargi da batanci kan Annabi Muhammadu (SAW).
Mahaifinsa shine Sheikh Nasiru Kabara, tsohon shugaban darikar Kadiriyya ta Afirka ta Yamma, kuma kanin Karibullah Nasiru Kabara, wanda ya gaji mahaifinsu.
Ya halarci makarantar ATC Gwale a Kano, kafin ya tafi Iraqi inda ya cigaba da karatunsa na addinin islama, duk da cewa ya yi mafi yawan karatunsa na a gaban mahaifinsa na tsawon shekara 25.
Abduljabbar ya shahara a matsayin mabiyin Qadiriyya kuma malamin Sunna a tsakanin al’ummar Musulmi a Najeriya, yana bin sahun mahaifinsa.
Abduljabbar ya danganta kansa da Shi’a
Amma a wata hira da ya yi da BBC, ya danganta kansa da Shi’a yana cewa: “Bayan bincike da nazari mai tsawo da na yi da kaina, na lura Shi’a sun fi hujja kwarara fiye da Sunni,” ya kara da cewa, “Ba zan damu idan idan ka kira ni dan Shi’a ba, amma zan damu idan ka kira ni Sunni.”
An dade ana zargin Abduljabbar da yin batanci da Annabi Muhammad da wasu sahabansa a karatunsa da maganganu da ya ke yi a bainar jama’a.
A cewar Abduljabbar, wasu hadisan Annabi da fitattun malaman addinin musulunci kamar su Anas Ibn Malik, Bukhari da Muslim suna zargin Annabi, wanda shi (Abduljabbar), ke cewa hadisan karya ne ko kuma akwai kurakurai cikinsu.
Gwamnatin Jihar Kano ta tsare Abduljabbar bayan malaman addinin musulunci daga kungiyoyin Izala, Salafiyya, Tijaniyyah da Kadiriyya sun yi korafi a kansa.
Sun ce sun sun ci karo da “wurare tara da Abduljabbar ya yi batanci ga Annabi a yayin karatunsa na bidiyo da murya, wanda suka yi amfani da su a matsayin hujja kan cewa Abduljabbar ya yi batanci ga Annabi Muhammad kuma idan ba a dauki mataki ba hakan zai janyo zubar da jini da tashin hankali a jihar.”
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta shiga cikin lamarin ta shirya mukabula tsakanin Abduljabbar da masu zarginsu, don a bashi damar gabatar da hujja kan abin da ya ke fada a wa’azinsa.
Mukabula tsakanin Abduljabbar da malamin Kano
A ranar 10 ga watan Yulin 2021, gwamnatin Kano ta shirya mukabala tsakaninsa da wasu malamai hudu a matsayin wakilai daga kungiyoyin Izala, Salafiyya, Tijjaniyya da Kadiriyya.
Farfesa Salihu Shehu daga Jami’ar Bayero ta Kano ne ya jagoranci mukabalar da Ma’aikatar Harkokin Addini na Kano ta shirya.
Bayan an kammala mukabalar, shugaban, Farfesa Shehu ya ayyana cewa Abduljabbar bai amsa ko tambaya daya ba da sauran malaman suka masa.
Ya ce, “Abduljabbar ya kauce wa tambayoyin ta hanyar bada bayanai da ba su ake nema ba kuma ko lokaci guda bai kawo hujja daga cikin littafai fiye da dari biyar da ya taho da su ba, duk da cewa yana da mataimaka da ke tallafa masa, yayin da sauran malaman sun bada hujoji tare da amsa tambayoyin Abduljabar kai tsaye.”
A ranar 17 ga watan Yulin 2021, an tsare Abduljabbar a gidan gyaran hali kan zargin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).
Tushe: News Brief Hausa