Tuesday, September 12, 2023

Karamar Yarinya Ta Sanya Kayan Amare, Ta Bukaci a Daura Masu Aure Da Mahaifinta

Manyan Labarai

Bidiyon wata karamar yarinya da ta nemi auren mahaifinta ya haifar da zafafan martani a dandalin soshiyal midiya.

Wata mai suna Nshimba Tshitende Re ce ta wallafa bidiyon yarinyar a TikTok inda aka gano ta sanye da farar doguwar riga irin na amare.

A cikin Bidiyon wanda tsawonsa bai wuce minti daya ba, yarinyar ta fito daga dakinta cikin shiga irin ta amare domin daurin auren.

Yarinyar ta ce mahaifinta take son aure

Miskila daya da aka samu shine cewa yarinyar ta bukaci a daura mata aure da mahaifinta ne wanda ko a mafarki hakan ba zai taba faruwa ba.

An kuma ganota sanye da wani takalmi wanda ya fi karfin kafarta kuma hakan ya ja hankali masu amfani da dandalin na TikTok bayan sun ci karo da bidiyonta.

Yayin da mahaifinta ke kokarin fahimtar abun da take so ayi, yarinyar ta bukaci a fara daurin auren ba tare da bata lokaci ba.

Mutane da dama sun yi tsokaci kan bidiyon

@viewsby_nc ta yi martani:

“Wai ji nayi ta ce “eh maigidana? Hadadden saurayi.”

@Karabo.nn ta yi martani:

“Don haka mu fara da ta fadi a karshe shine ya fi jan hankalina.”

@Zimkhitha Cleo Ntuli ta ce:

“Za mu yi aure a yanzu. Har ma ta san cewa duk kun dade kafin ku yi mata tambayar.”

@Mbali Cele ta yi martani:

“Ba dai saurayin ya shiga rudu ba yayin da ita ta shirya ma didiman.”

@Mantsundu ta yi martani:

“Duk yara mata suna fadawa tarkon soyayyar mahaifansu maza. Nima mahaifina na so na aura.”

MASALA ta ce:

“Lallai yarinyar na ganin irin tarairayar da mahaifiyarta ke samu daga mijin ba nan bane don haka ita ma take son samun girbi, sarkin wayo.”

NB Tlou ta ce:

“Bata son jin wani uzuri, don haka ta shirya ma ranar da kanta…Don haka ku mu fara abun da ya tara mu.”

mhlangomuhle ya yi martani:

“Ku yi sauri shi ya fi daukar hankalina.”

A wani labarin kuma, wasu mata da miji sun dankara hadadden gida sannan suka tare abunsu ba tare da sun zuba kayan daki ba.

Matar ta ce kayan dakin zai iso kasar ne a cikin shekara mai zuwa don haka suka koma ciki abunsu a haha.

Duba nan: