Tsohon SGF, Babachir Lawal, ya musanta raÉ—e-raÉ—in dake yawo cewa ya jingine Peter Obi, ya koma bayan É—an takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
Tsohon Sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal, ranar Litinin, ya jaddada cewa ba zai goyi bayan ɗan takarar ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar ba a zaɓen 2023, rahoton Punch.
A cewarsa burin Atiku bai yi dai-dai da tsarin da ya dace na sauya gwamnati ba domin zai kasance daga shugaban ƙasa bafullatanin Musulmi zuwa wani shugaban Bafullatani kuma Musulmi.
Lawal ya yi wannan karin hasken ne yayin da yake martani kan rahoton da ya karaɗe soshiyal midiya cewa ya jingini ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi, ya koma gidan Atiku.
DUBA WANNAN:Â Mambobin Jam’iyyar PDP Sun Sauya Sheka Zuwa NNPP A Gombe
Ya gargaɗi cewa idan har Atiku ya kai ga nasara alama ce dake nuna ƙabila ɗaya ta mamaye sauran, kamar yadda rahoton Punch ya tabbatar.
A wata sanarwa da Lawal ya fitar ya jaddada goyon bayansa ga mai neman zama shugaban Æ™asa a inuwar LP, Peter Obi, inda yace, “Ina nan a matsayin É—an amutun Obi.”
Tsohon SGF yace:
“Yanzu nake gani wani labari na yawo cewa na bar tafiyar Peter Obi na koma aiki da Atiku Abubakar. Babu Æ™ansin gaskiya a wannan zance, ban taba ko da tunani ko tantamar shiga PDP ba domin ina kallon jam’iyyar a matsayin mafi muni da ta haÉ—a yan kanzagi da masu kwaÉ—ayin mulki don kansu.”
“Baya ga haka ma, na tsinci kaina a wata shekara da na sha fama da faÉ—i tashin takaddama da Fulani waÉ—anda ke tura dabbobinsu su shiga cikin gonata su cinye mun amfani kusan duk shekara.”
DUBA WANNAN:Â Daruruwan Mambobin PDP da Jiga-Jigai Sun Koma APC a Katsina
“Wannan matsalar ba ni kaÉ—ai bane, haka suke wa dattawan mu da sauran manoma a sassan arewacin Najeriya. Duk suna haka ne su É“ata mana amfanin gon saboda Æ™eta kuma abin mamaki shugabanninsu dake cikin gwamnati sun kama bakinsu sun yi shiru.”
“Bugu da Æ™ari, ni ina ganin sauya gwamnati daga Fulani Musulmi zuwa wani Fulani Musulmi ya fi muni fiye da takarar Musulmi da Musulmi. Yana wakiltar Kabila É—aya ta mamaye komai, ta latse sauran kabilu.”
“Ina nan a matsayin É—an a mutun Peter Obi, dum wani labari da ba haka ba karya ne.”
Tushe: News Brief Hausa