Wednesday, May 29, 2024

Mambobin Jam’iyyar PDP Sun Sauya Sheka Zuwa NNPP A Gombe

Manyan Labarai

Dan takarar gwamnan jihar Gombe a inuwar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party watau NNPP, Khamisu Mailantarki, ya karbi shugabanni da mambobin ƙungiyar Sardauna Dawo-Dawo, ƙungiyar magoya bayan jam’iyyar PDP.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ya karbi masu sauya shekar waɗanda suka haɗo kayansu suka bar PDP zuwa NNPP a Gombe ranar Jumu’a.

Daruruwan masu sauya shekar sun samu tarba da hannu biyu da kuma maraba daga shugaban NNPP na jihar, Abdullahi Maikano.

Kungiyar Sardauna Dawo-Dawo, ta sauya sunanta nan take bayan tabbatar da sauya sheƙa a hukumace zuwa Mailantarki Movement.

A cewar ƙungiyar ta yanke komawa bayan ɗan takarar gwamna a NNPP, wanda ya kasance, “Matashi mai jini a jika, wanda ya cancanta kuma kowa na shi ne babu banbamci tsakanin mutane.”

Shugaban tawagar masu canza shekar, Muhammad Makson, yace Mailantarki mutum ne da an jaraba shi kuma an gani a ƙasa, kuma yana da kwarewa da salon kawo karshen matsaloli da ƙalubalan da suka baibaye Gombe.

A jawabinsa, Makson ya ce:

Sauya ra’ayinmu da tsame kanmu daga goyon bayan PDP wata matsaya ce da bakin mu ya zo ɗaya a kanta. Baki ɗayan mu muka yanke shawari kana muka mara wa ɗan takarar NNPP baya saboda mu sami kagoranci na gari.”

Muna da yakinin cewa Mailantarki na da halayya masu kyau kuma yana da dabarun ceto jihar daga APC mai mulkim kama karya.”

Akalda adadin mutum nawa ne suka koma jam’iyyar Kwankwaso?

Ya bayyana cewa ƙungiyar na da shugabanni 2000 da mambo 22,000 a dukkanin sassan ƙananan hukumomin jihar Gombe.

Da yake maraba da masu sauya shekar, Khamisu Maintarki ya basu tabbacin cewa za’a tafi da su a dukkanin harkokin jam’iyya ba bu nuna wariya.

“Musamman yanzun da aka fara yakin neman zaɓe kuma da ikon Allah NNPP Zata samu nasara a babban zaɓe mai zuwa.”

Ya roki dubbanin mutane da suka haɗa magoya baya ga jam’iyyar, waɗanda zasu goyi bayan ‘yan takara baki ɗaya.

“Ba wai sai  NNPP ta ɗauko daga tushe ba sannan zata iya lallasa jam’iyyar APC da mutane suka gaji da ita, zamu kafa gwamnati da kowa kuma mu jawo kowa idan aka zaɓe shi muka ci mulki a 2023.”

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: