Wednesday, March 1, 2023

Daruruwan Mambobin PDP da Jiga-Jigai Sun Koma APC a Katsina

Manyan Labarai

Jam’iyyar APC mai mulkin jihar Katsina ta samu gagarumin karin goyon baya daga wasu dandazon mambobin jam’iyyar PDP gabanin babban zaɓen 2023.

Daruruwan mambobin jam’iyyar PDP a ƙaramar hukumar Mashi ta jihar Katsina ne suka tattara yanasu yanasu suka koma APC mai mulki a cewar rahoton PM News.

Daraktan yaɗa labarai na kwamitin yakin neman zaben APC a jihar Katsina, Alhaji Ahmed Abdulkadir, ne ya sanar da haka yayin zanta wa da manema labarai a Birnin Katsina.

Yace masu sauya shekar sun samu tarba mai kyau daga shugaban jam’iyyar APC na jiha, Alhaji Sani Daura, a wurin taron kamfe na ɗan takarar gwamna a 2023, Dakta Dikko Radda, wanda ya gudana a Mashi.

A jawabinsa yace:

“Radda ya fara Kamfe daga Baure a shiyyar Katsina ta arewa, mazabar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bayan kaddamar da farawa a ƙaramar hukumar Faskari. Zuwa yanzu ya karaɗe 6 cikin kananan hukumomi 12 da suka haɗa shiyyar Daura.”

“Ya ziyarci gundumomi sama da 60. A Daura ya ziyarci shugaban ƙasa ya gaya masa ya zo ne ya faɗa masa halin da mutane ke ciki da zummar haɗa hannu wajen tattara bangarorin da ya dace a maida hankali idan Allah ya ba shi mulki.”

“Mai girma shugaban ƙasa ya yaba da kokarin dan takarar gwamnan kuma ya nuna masa kwarin guiwar cewa zai iya lashe zabe mai zuwa.”

Jam’iyyar APC ta karbi mulkin jihar Katsina ne a shekarar 2015 lokacin da tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Aminu Bello Masari, ya lashe zaben gwamna.

A shekara mai kamawa watau 2023 ne zango na biyu na mulkin gwamna Aminu Masari zai kare sai dai jam’iyyarsa ta APC na fatan ci gaba da jan zare wajen samun nasara a zaɓe.

Dakta Dikko Radda, wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC kuma ya zama sahihin ɗan takarar gwamna, zai fafata da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: