Thursday, November 7, 2024

Zakulo Gaskiya: Shin Matasan Kaduna Sun Yi Zanga-Zangar Adawa Da Takarar Tinubu?

Manyan Labarai

Wani bidiyo na dikaka 10 da ake zargin mutane ne ke yin zanga-zangar kin nuna goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bazu a Twitter.

Rubutun da ke jikin bidiyon ya yi ikirarin cewa fusatattun matasa ne a karamar hukumar Birnin Gwari na Jihar Kaduna ke zanga-zangan nuna rashin goyon bayan takarar Tinubu, da cewa ba za su zabe shi ba a 2023.

 

Wasu rubutun sun ce, “Fusatattun matasan karamar hukumar Birnin Gwari na yin ihun ‘Bamayi’ ga Asiwaju Bola Tinbu a fadar sarki a daren yau. Jagaban ya shiga wahala shi yasa dole mu zabi Peter Obi.”

Wani rubutun da aka fitar da bidiyon ya ce, “Fusatattun matasan karamar hukumar Birnin Gwari a Kaduna suna ihun ‘Bamayi’ ga Asiwaju Bola Tinubu a fadar Sarki a daren jiya don nuna kin amincewa da tursasa musu dan takarar shugaban kasa na APC.”

Wannan bidiyon da aka wallafa ya yi farin jini sosai, har ya sa Birnin Gwari ya yi tashe a Shafin Twitter na Najeriya a ranar Talata.

Tantancewa

Don tantace sahihancin wannan ikirarin, an yi nazarin hotuna daya bayan daya na bidiyon kuma hakan ya nuna bidiyon ya fara fitowa a intanet ne a ranar 12 ga watan Disamban 2022 a fadar sarkin Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Amma, wasu maganganu da aka yi karkashin bidiyon ya nuna taron ba shi da alaka da Tinubu duk da cewa yana fadar lokacin da abin ya faru.

Wani mazaunin Birnin Gwari, Ibrahim Jigo, wanda ya halarci taron, ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa matasan na zanga-zanga ne kan kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan, kan wani magana da ya yi kan batun tsaro a jihar.

Ya ce:

“Mutanen suna da matsala ne da kwamishinan saboda dalilai biyu zuwa uku amma babban matsalar shine mutanen garin ba su jin dadin rahotanninsa kan tsaro. Ya kan rage girman abin da ya faru.

“Wasu masu zanga-zangan yan kasuwa ne wadanda aka kwace wa babura kuma ba a dawo musu da shi ba. Sun dora laifin kan kwamishinan da suka ce shi yasa aka kwace musu kayayakinsu. Abin da matasan ke cewa shine ‘Bamayin Samuel Aruwa’ ba Bamayin Tinubu ba kamar yadda wadanda suka wallafa bidiyon ke nufi.”

Hukunci: Karya ne

Kammalawa: Bisa la’akari da binciken, Daily Trust na iya tabbatar da cewa ikirari na cewa matasa a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna sun yi zanga-zangar nuna adawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ba gaskiya bane kuma yaudara ne.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: