Kano – A halin yanzu an tsaurara tsaro a ciki da kusa da Kofar Nasarawa kan hanyar fadar sarki a yayin da babban kotun shari’a a yau za ta yanke hukunci kan shari’ar tuhumar batanci ga Annabi da ake yi wa malami, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Hukuncin na zuwa ne watanni 15 bayan fara shari’ar na malamin addinin islaman mazaunin Kano a gaban babban kotun shari’a da ke zamanta a Kofar Kudu karkashin jagorancin Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, Daily Trust ta rahoto.
An tuhumar Kabara ne da laifuka masu alaka da batanci ga manzon tsira Annabi Muhammadu (SAW) wanda hakan na iya tada rikici a tsakanin al’umma.
Tushen shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara Nasiru
Gwamnatin jihar Kano ne ta gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu a watan Yulin 2021.
Daily Trust ta lura cewa a safiyar ranar Alhamis an tura jami’an tsaro yankin kusa da fadar sarkin Kano inda kotun ya ke.
Misalin karfe 8.51 na safiyar yau, an kawo malamin cikinn kotu tare da jami’an tsaro na gidan gyaran hali.
Yan jarida, kungiyoyin kare hakkin bil adama da lauyoyi tuni sun samu wuri sun zauna a kotu suna jiran a fara shari’ar.
An hana ababen hawa bin hanyar
Wani mazaunin unguwar Kofar Nasarawa da News Brief Hausa ta samu ji daga bakinsa ya ce an hana motocci da babura bin hanyar a halin yanzu.
Matashin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya kuma ce mutanen unguwa suna nan sun kasa kunnuwa suna jiran su ji irin hukuncin da kotu za ta yanke wa malamin bayan lokaci mai tsawo ana shari’ar.
Tushe: News Brief Hausa