Wednesday, November 6, 2024

Yadda Lashe Zaben Trump ya daga Dukiyar Elon Musk da $13bn

Manyan Labarai

KANUN LABARI

  • Bayan nasarar zaɓen Donald Trump a Amurka, Elon Musk ya samu riba mai tsoka da ta kai dala biliyan 13
  • Nasarar Trump ta taimaka wa Musk wajen ƙara darajar hannayen jarin Tesla, wanda ya sa darajarsu ta ƙaru zuwa miliyan 411 a cikin lokaci kaɗan
  • Elon Musk ya ba wa kamfen ɗin Trump gudunmawar kuɗi mai yawa da ya kai dala miliyan 119
  • A matsayin babban mai goyon bayan Trump, Musk ya yi hira ta musamman da shi a manhajar X kafin zaɓen
  • Kasuwancin Musk, musamman kamfanoninsa na Tesla da SpaceX, suna cin gajiyar haɗin gwiwar gwamnati

Kasar Amurka – Awanni kaɗan bayan nasarar Donald Trump a zaɓen shugaban ƙasa na Amurka, attajiri Elon Musk ya samu riba mai tsoka.

Elon Musk, wanda shi ne shugaban kamfanin X (Twitter), ya samu Karin kuɗaɗe sama da dala biliyan 13 ($13bn) bayan nasarar dan takarar da yake marawa baya, Trump.

Kamfanin labaran CNN ya ruwaito cewa, nasarar Trump ta kasance abin alheri ga hannun jarin kamfanin Tesla mallakar Elon Musk.

Donald Trump da Elon Musk
Arzikin Elon Musk ya karu da $13bn | Hoto: GettyImages

Wannan nasara ta taimaka wajen ƙara darajar hannayen jari na Tesla da aka ƙiyasta adadin su ya kai kusan miliyan 411, wanda ya ƙara wa Musk ribar da ta kai dala biliyan 13 a cikin ɗan lokaci kaɗan.

Kafin zaɓen, rahotanni sun nuna cewa Elon Musk ya ba wa gangamin kamfen ɗin Trump gudunmawar kuɗi mai tsoka da ya kai dala miliyan 119 ($119m).

Wata majiya ta bayyana cewa babu wani attajiri ko babban ɗan kasuwa da ya goyi bayan Trump kamar Elon Musk a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar.

Wannanalaka tsakanin Musk da Trump ya bayyana ta hanyar irin gudunmawar kuɗi da lokacin da Musk ya ke bayarwa ga yakin neman zaɓen Trump.

Ba wai kawai ya tsaya a gudunmawar kuɗi ba, har ma ya yi hira ta musamman da Trump a manhajar X kafin zaɓen, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi Amurka da harkokin kasuwanci.

Haɓakar arzikin Elon Musk, a cewar masana, ya samu ne ta hanyar ribar kamfanoninsa na Tesla da SpaceX waɗanda suka jima suna cin gajiyar ƙarin tallafi da kwangiloli daga gwamnatocin Amurka daban-daban.

Kamfanonin nasa suna samar da kayayyaki da ayyukan da suka shafi fasaha da kera motoci na zamani, wanda hakan ke jawo musu haɗin gwiwa da goyon baya daga gwamnati.

Duk da irin wannan goyon baya da Musk ke bayarwa ga Trump, wasu masu sukar lamiri na kallon wannan alaƙa a matsayin wata dabarar kasuwanci da Musk ke amfani da ita don ya samu gagarumar riba daga kuɗin tallafi da kasuwanci da gwamnatin Trump za ta samar wa kamfanoninsa.

Duba nan: