Thursday, May 30, 2024

Buhari Ya Yi Martani Kan Kisar Gillar Da Aka Yi Wa Yan Najeriya 16 A Burkina Faso

Manyan Labarai

FCT Abuja – Buhari ya tabbatar da za ayi adalci ga ‘yan Najeriya 16 da aka kashe a Burkina Faso ta hanyar aiki da ma’aikatar harkokin waje da ofishin jakadancin Nigeria a burkina faso.

 

Garba Shehu, babban mai bada shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, rahoton Daily Trust.

 

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

 

Wasu ‘yan kungiyar Jam’iyyatu Ansariddeen Attijaniyya ta Najeriya 16 ne wasu sojojin kasar Burkina Faso suka yi wa kisan gilla a lokacin da suke gudanar da tattaki zuwa kasar shugabansu Sheikhul-islam Ibrahim Niasse a kasar Senegal.

 

Sayyidi Yahaya, sakataren kungiyar Islama ta kasa, ya bada rahoton cewa an zabo mambobin kungiyar ne aka harbe su har lahira a wani yanayi na nuna rashin tausayi.

 

Buhari ya mayar da martani kan lamarin na ranar Litinin, inda ya ce ya yi matukar bakin ciki da labarin kisan da aka yi wa wasu mahajjatan Najeriya da ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Kaolak na kasar Senegal.

 

Duba Wannan: Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Ya Fice Daga APC Zuwa PDP

 

Shugaban ya mika ta’aziyyarsa tare da nuna damuwarsa ga lafiyar sauran ‘yan Najeriya mazauna yankin.

 

Ya kuma kara da cewa, ma’aikatar harkokin wajen kasar da ke aiki ta ofishin jakadancin Najeriya da ke Burkina Faso, na hada kai da hukumomin kasar domin gudanar da bincike kan lamarin.

 

Shugaban ya bayyana cewa za a dauki matakan da suka dace don hukunta wadanda suka aikata laifin.

Duba nan: